1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Tattalin arziki

Yakin Ukraine ya sa farashin fetur na karuwa a Afirka

Silja Fröhlich ZMA/MAB | Martina Schwikowski ZMA/MAB
March 2, 2022

Kasashen Afirka da ke Kudu da hamadar Sahara na fuskantar mawuyacin hali na tashin farashin man fetur, a daidai lokacin da mamayar da Rasha ta yi wa Ukraine ke kara tsananta farashin makamashin gas a kasuwannin duniya.

https://p.dw.com/p/47ugw
Uganda | Total Tankstelle
Hoto: Hajarah Nalwadda/AP Photo/picture alliance

Legos da ke zama cibiyar kasuwancin Najeriya da kuma ya fi yawan al'umma na cikin rudani sakamakon karancin man fetur. Fada kan barke tsakanin direbobi da suka dauki kwanaki suna jerin gwano a kan titi a gidajen sayar da man, wanda kan tare sauran masu son amfani da hanyar. Masu motoci musamman a manyan biranen Najeriyar dai, kan dauki sao'i masu yawa, wasu lokuta har kwanaki a kokari na jiran tsammanin samun mai.

 Joy Agbonifo da ke cikin layin jiran man ta kasa boye takaicinta. Ta ce "Samun man fetur kamar hakar zinare ne, mun shafe sa'o'i muna neman shi kuma babu tabbacin cewa za ka samu wannan man. Mutane da yawa suna sayen man fetur din kuma su boye don sayar da shi a farashi mai tsada, abin da Najeriya ta zama kenan."

An yi ta zanga-zanga kan man fetur a Najeriya

Nigeria Gwagwalada Proteste gegen hohe Benzinpreise
Tun kafin yakin Ukrainen an yi ta zanga-zanga kan tsadar man fetur a Najeriya.Hoto: AFOLABI SOTUNDE/REUTERS

Sama da makonni uku kenan ake fama da karancin man fetur a tarayyar ta Najeriya. Lamarin da ya samo tushe bayan da gwamnatin kasar ta tsayar da shigo da man da ta ayyana a matsayin "gurbatacce". Yawancin dillalan man fetur dai sun kara farashi fiye da Naira 165 da aka yarda a hukumace, batu da ya sa ake kallon matsalar tamkar wadda aka kirkira da gangan. Sai dai a cewar masanin tattalin arziki kuma tsohon farfesa a jami'ar Amadu Bello da ke Zaria Abdul-Ganiyu Garba, wannan matsala ce da ta yi wa duniya kamun kazar kuku ba Najeriya kadai ba...

Ya ce "Halin da ake ciki yanzu ya shafi duniya baki daya, saboda ko a sauran kasashen yammacin Turai, farashin makamashin gas ya hau sosai, musamman tun bayan annobar da duniya ta fada a baya, har yanzu ana kokarin farfadowa.  Daura da haka, yawancin kasashen da ke kudu da hamadar Sahara masu arzikin albarkatun kasa a zahiri ba su alkinta albarkatun ba, ta yadda za su iya dogaro da kansu a yanayi na sauyi  bisa tsarin darajarsu."

Takunkumi kan Rasha bai shafi makamashi ba

Russland Symbolbild Ölförderung
A yankin Tatarstan ne ake hako man fetur a kasar RashaHoto: picture-alliance/dpa/Y. Aleyev

Yakin da Rasha ta kaddamar a kan Ukraine ya sake jefa duniya cikin wadi na tsaka mai wuya a fannin makamashi. Ita dai Rashar na zama ta biyu a jerin kasashe masu arbarkatun danyen mai a duniya. Duk da cewar takunkuman da aka sa mata ba su shafi bangarenta na fitar da mai ba, akwai fargabar sannu a hankali za a kai ga taba harkokinta na sarrafa mai. Mambobin hukumar makamashi ta duniya, ciki har da kasa mafi girma wajen fitar da mai watau Amirka, sun amince da sakin karin ganga miliyan 60 na danyan mai daga cikin na ajiye. Sai dai matakin bai sa  kwalliya ta iya biyan kudin sabulu ba.

Kasahen Afirka dai tamkar sun fi jin radadin tsada da ma karanci na man fetur da makamashin gas. Matsalar da ta zama tamkar ruwan dare a Najeriya, kasar da ta fi kowace fitar da danyan mai zuwa ketare a nahiyar Afirka. Sai dai matsalar ba ta tsaya a Najeriya kadai ba, hatta a Burkina Faso farashin man ya karu da wajen kaso 8%. Kazalika Afirka ta Kudu da Jamhuriyar Dimukaradiyyar Kwango da Kenya. Al'ummar Burundi na cikin fargabar tashin farashin kayan abinci da ke shiga kasar wanda a kan danganta da farshin man fetur.

Bayan Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya dai, Zimbabuwe da Senegal da Burundi sun kasasnce kasashen Afirka da suka fi kowanne tsadar man fetur.