Faransa za ta sauya tsarinta na soja a Sahel | Labarai | DW | 26.11.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Faransa za ta sauya tsarinta na soja a Sahel

Faransa ta ce za ta kawo sauye-sauye ga ayyukan sojojinta a kasashen Gabas ta Tsakiya da kuma yankin Sahel, a cewar babban hafsan hafsoshin kasar.

Yayin wata hira da aka yi da shi a wannan Lahadin babban hafsan hafsoshin kasar Faransa Janar François Lecointre ya ce dangane da rundunar sojojin kasar ta Faransa a yankin Sahel ta Barkhane mai kumshe da sojoji 4000 za su rubunya tallafin da suke bai wa kawayensu na kungiyar G5 Sahel, ta yadda za ta iya zama mai cin gashin kanta. Ya ce Faransar za ta yi kokarin rage sojojin da take da su a kasa.

Kungiyar G5 Sahel da ta kumshi kasashen Mauritaniya, Mali, Burkina Faso, Chadi da kuma Nijar ta girka tata runduna ta hadin gwiwa da za ta lura da iyakokin kasashen a wani mataki na yakar ayyukan 'yan jihadi da sauran masu safarar miyagun kwayoyi a yankin na Sahel.