1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Maduro ya gagara kiran zabe

Yusuf Bala Nayaya
January 30, 2019

Faransa dai da wasu mambobi na Kungiyar EU sun bayyana cewa nan da ranar Asabar za su karbi jagoran adawa Juan Guaido a matsayin shugaba halastacce.

https://p.dw.com/p/3CTPd
Venezuela, Caracas: Nicolas Maduro hält eine Ansprache
Hoto: Reuters/Miraflores Palace

Faransa a wannan Laraba ta bayyana cewa alamu sun nunar da cewa Shugaba Nicolas Maduro ba shi da niyya ta kiran gudanar da zabe don haka ministocin harkokin wajen Turai za su dauki mataki na gaba a zaman da za su yi Bucharest a ranar Alhamis. Faransa dai da wasu mambobi na Kungiyar EU sun bayyana cewa nan da ranar Asabar za su karbi jagoran adawa Juan Guaido a matsayin shugaba halastacce muddin Maduro ya gaza kiran gudanar da zabe a kasar. Wasu 'yan siyasa a Jamus ma dai sun nemi a yi sabon zaben a Venezuela.

Wasu rahotanni sun nunar da cewa an kama wasu 'yan jarida Faransawa masu aika rahoton rikicin siyasa daga Venezuela. Acewar ofishin jakadancin Faransa yana aiki wajen ganin an saki 'yan jaridar da aka kama a diflomasiyance kamar yadda majiyar da ta ba da rahoton ta nunar a wannan Laraba.

Tuni dai ofishin jakadancin na Faransa ya nemi a ba da kariya ga 'yan jaridar bayan da ya samu labarin kama su. Har ila yau ya bukaci  a mutunta yarjejeniyar Vienna a kuma ba su dama ta ganawa da jami'ai.