Fafutukar samun shugabancin Najeriya a 2015 | Siyasa | DW | 30.12.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Fafutukar samun shugabancin Najeriya a 2015

Mutane tara ne yanzu haka ke zawarci kujerar shugabancin Najeriya a zabukan gama-gari na watan Fabrairun shekarar ta 2015 da muke dab da shiga.

Samun ‘yan takara da ke neman shugabancin Najeriya har guda tara da zasu fafata a zaben na 2015 na nuna share fagen tunkarar juna ta hanyar neman kuru'u daga ‘yan Najeriyar sama da milyan 70 da suka kai shekarun jefa kuri'a, wadanada tsarin mulkin kasar ya basu damar su darje domin rarrabe aya da tsakuwa wajen zaben wanda zasu dankawa ragamar jagorantarsu na tsawon shekaru hudu masu zuwa.

Sierra Leone Wahlen 2007

Kimanin mutane miliyan 70 ne a Najeriya za su kada kuri'a a zabukan 2015.

Ko da yake hankakula sun fi karkata a kan shugaban Najeriya Goodluck Jonathan na jam'iyyar PDP da Manjo Janar Muhammadu Buhari mai ritaya na jamiyyar adawa ta APC, amma akwai sauran ‘yan takara da suka hada da Chekwas Okorie na jamiyyar UPP da Cif Martin Onovo na NCP sai kuma Alhaji Ganiyu Oseni na jamiyyar APP da kallabi tsakanin rawuna watau Comfort Oluremi Sonaiya ta jamiyyar Kowa Party.

Wahlen Nigeria Attahiru Jega

Hukumar zaben Najeriya ta ce ta shirya don ganin an gudanar da sahihin zabe.

Tuni dai masu sharhi a fagen siyasar Najeriya suka fara tsokaci a kan yadda suke kalon fafatawar da za'a yi a tsakanin ‘yan takarar. Malam Buhari Jega masani ne a siyasar Najeriyar ya kuma ce "zaben da za a yi zabe ne da ya zo da wani salo da muke ganin ya nuna cewar an fara dan manyanta a harkar dimokradiyya."

A daidai wannan lokacin dai wakilan jam'iyyun siyasar Najeriyar na ta kai da komowa domin cimma wa'adin na hukumar zaben domin fuskantar zaben na 2015. Barrister Kabiru Umaru Dodo na daya daga mutanen da wakilinmu Uwais Abubakar Idris ya iske a hukumar zaben ya kuma shaida masa cewar "A yadda hukumar zabe ke tafiya a yanzu duk wanda ke tunanin ya na da wata hanyar da zai bi ya ci zabe ba wannan ba, to ya sauya tunani duba da irin shirin da ta yi."

Symbolbild Nigeria Polizei

Rundunar 'yan sanda ta ce ta shirya magance tashin hankali a zaben 2015.

Nan da 'yan kwanakin da ke tafe ne dai hukumar zaben ta Najeriya za ta buga daukacin sunayen mutanen da za su yi takara a zabukan na 2015 batun da ya sanya tambayar halin da ake ciki kan wa'adin sauya 'yan takara. Mr. Nick Dazzan da ke magana da yawun hukumar ya bayyana cewar "yanzu dai muna karban sunayen amma zuwa karfe goma sha biyu na yau (301.12.14) zamu bar karbar wani sauyi ko sunayen dan takara''.

Yanzu haka dai 'yan Najeriya da sauran jama'a na kasashen Afirka da ma duniya baki daya sun zuba idanu don ganin irin yadda zaben zai kasance da ma alkiblar da kasar za ta dauka bayan an girka gwamnati a cikin watan Mayun shekara mai kamawa.

Sauti da bidiyo akan labarin