EU ta mike kan makomar ′yan gudun hijira | Siyasa | DW | 24.09.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

EU ta mike kan makomar 'yan gudun hijira

Tsawon sa'o'i bakwai shugabannin kasashen kungiyar tarayyar Turai EU suka kwashe suna tattaunawa kan yadda za su tinkari matsalar 'yan gudun hijira da ke kwararowar nahiyar ta Turai.

Belgien EU Gipfeltreffen Flüchtlingskrise

Shugabanni daga kasashen EU yayin taro kan 'yan gudun hijira a Beljiyam

Da kudan kudade da kuma kwararan shirye-shirye, shugabannin sun kuduri aniyar magance wannan matsala tun daga tushenta. Shugabannin na EU sun dauki lokaci mai tsawo suna tattaunawa game da rikicin 'yan gudun hijirar ba tare da sun kawar da ainihin takaddamar da ke tsakanin kasashen gabashi da na yammacin kasashen na Turai game da raba yawan kason 'yan gudun hijirar ba. Sai dai shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta ce taron ya gudana cikin yanayi kyakkyawa tana mai cewa an amince a hada karfi da karfe waje guda don tinkarar kalubalen da ke gaba, inda ta nuna muhimmancin ganawar da aka yi tsakanin shugabannin na Turai.

Musayar yawu

Brüssel - EU Gipfel Flüchtlinge

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Markel

"Na gamsu da sakamakon taron. Ko da yake mun san cewa ba a samar da dukkan ka'idojin da ake bukata na warware matsalar 'yan gudun hijirar ba, amma muna kan turbar da ta dace. Muhimmin abu shi ne taron ya ba mu damar musayar yawu a kokarin samun fahimtar juna a kan batun da ke gabanmu."

Taron na shugabannin kasashen na EU ya ware Euro miliyan dubu biyu don inganta tallafi ga 'yan gudun hijirar Siriya da ke kasashe makwabta. Sannan rabin wadannan kudade za a ba wa hukumar samar da abinci ta duniya da hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya da dukkansu biyu suka shafe watanni suna kukan karancin kudi. Ita ma kasar Turkiya an ware mata wani kaso na kudaden, yayin da su ma kasashen Lebanon da Jodan za su samu wasu miliyoyin Euro daga kudin tallafin. Miliyoyin 'yan gudun hijirara Siriya dai ne suka samu mafaka a makwabtan kasashen. Adadin da zai karu a fadar shugaba Angela Markel.

Hankali zai karkata kan iyakoki

Flüchtlinge / EU-Gipfel / Brüssel / Jean-Claude Juncker und Donald Tusk

Jean-Claude Juncker da Donald Tusk a taron Brüssel

"A bayyane yake cewa yawan 'yan gudun hijira zai karu. Saboda haka wajibi ne mu yi wa manufar bude kofofinmu kwaskwarima. Yanzu za mu mayar da hankali wajen kare kan iyakokinmu na waje tare kuma da kara yawan taimako ga 'yan gudun hijira da kuma kasashe makwabtanmu. A kan haka shugabanin EU sun amince su kara yawan taimako ga Lebanon da Jordan da Turkiya da kuma sauran kasashe makwabta."

Shi ma shugaban hukumar tarayyar Turai Jean-Claude Juncker bayyana farin cikinshi ya yi game da sakamakon taron.

Zoran Milanovic Kroatien Niederlande Mark Rutte Großbritannien David Cameron EU Treffen Flüchtlingskrise Migration Brüssel Belgien

Shugabanni mahalarta taron EU

"Muhimmin abu gare ni shi ne amincewar da majalisar ta yi na ba wa hukumominta da kuma gwamnatoci umarni da su gaggauta aikin kan bukatun da hukumar tarayyar Turai ta gabatar. Abin da muke yi ke nan kuma za mu yi aiki kan muhimman ka'idojin da wannan shirin aiki ya kunsa."

EU din dai ba ta yi bayani kan bukatar karfafa tsaro a kan iyakokinta na waje ba. Sai dai hukumar ta EU za ta gabatar da wata shawara kafin karshen wannan shekara kan yadda tsarin kare kan iyakokin bai daya na tarayyar Turai zai kasance.

Sauti da bidiyo akan labarin