1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

EU ta bukaci a mutunta yarjejeniyar Minsk

Yusuf BalaFebruary 20, 2015

Jamus da Faransa sun jaddada bukatar da ke akwai na ganin an mutunta yarjejeniyar zaman lafiya da aka kulla tsakanin gwamnati da 'yan awaren Ukraine wacce ke tangal-tangal.

https://p.dw.com/p/1EfGq
Frankreich Deutschland Angela Merkel bei Francois Hollande in Paris
Hoto: Getty Images/T. Chesnot

A daidai lokacin da sojan 'yan aware da ke samun goyon bayan kasar Rasha ke murnar samun nasarar kara fadada yankin da suke da iko da shi, a bangare guda kuma ana ci gaba da musayar makaman atilare tsakanin dakarun 'yan tawayen da na gwamnati. Lamarin da ya sa shugabar gwamnatin Jamus Angela Markel ke cewa ba za su yi kasa a gwiwaba.

"Abubuwan da aka cimma a birnin Minsk a aiwatar da su yanzu, duk da cewa aiwatar da yarjejeniyar ta watan Satimba na da wahalar aiwatarwa saboda yanayin da aka samu kai amma abin da na sani shi ne dole a ci gaba da bada himma wajen ganin an cimmata, dan kaucewa kwarar da jini, saboda haka dole a aiwatar da tsagaita wutar a janye manyan kayan yaki a kuma yi musayar firsinoni"

Shi ma dai shugaba Francois Holland na Faransa tamkar shugabar gwamnatin ta Jamus Angela Merkel ya ce dole a tabbatar da ganin an aiwatar da wannan yarjejeniya.

Jami'an gwamnatin kasar ta Faransa sun bayyana cewa ministocin harkokin wajen Faransa da Ukraine da Rasha da Jamus zasu gana a birnin Paris a ranar Talata mai zuwa dan tattaunawa kan rikicin na Ukraine.