1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Rikice-rikiceBurkina Faso

EU na shirin sake samun tagomashi a Afirka ta Yamma

Nikolas Fischer LMJ/MAB
April 1, 2026

Yayin da gwamnatocin mulkin soja na Afirka ta Yamma ke karfafa hulda da Rasha da Chaina tare da mayar da kasashen Turai saniyar ware, kungiyar EU na ganin cewar lokaci ya yi da za a cimma yarjejeniyar da kowa zai amfana.

https://p.dw.com/p/5BVAE
Kungiyar EU ta saba gudanar da taro da kasashen Afirka don fahimtar juna
Kungiyar EU ta saba gudanar da taro da kasashen Afirka don fahimtar junaHoto: Michael Kappeler/dpa/picture alliance

Tsakanin shekara ta 2020 zuwa 2023, sojoji sun kifar da gwamnatocin da aka zaba karkashin tsarin dimukuradiyya a kasashen Mali da Burkina Faso da kuma Jamhuriyyar Nijar. Hakan ya shafi huldarsu da kasashen ketare, inda suka janye jikinsu daga kasashen Turai. Sannan daga bisani sun kulla alaka da kasashen Rasha da Chaina, sai kuma Amurka karkashin mulkin Shugaba Donald Trump da ke kara kulla alaka da gwamantocin mulkin soja. 

Karin bayani: Nijar da EU na neman ja wa ta’addanci birki a Sahel

Sai dai har yanzu ba ta sauya zani ba, saboda kungiyoyin 'yan ta'adda masu ikirarin jihadi na ci gaba da tayar da hankulan mazauna kasashen uku. Hannun agogo ya koma baya, in ji Gidauniyar Kimiyya da Siyasa ta Jamus Stiftung Wissenschaft und Politik (SWP) cikin wani nazari da ta fitar. Gidauniyar ta ce, duk da kayyadajjen tasirin da nahiyar Turai ke da shi a yanzu ya zama wajibi ta fito da wani tsari da zai taimaka wajen dakile kara ta'azzarar al'amura.

Kaja Kallas: "Dole ne ayyukan su ci gaba da wanzuwa a Afirka"

Babbar jami'ar hulda da ketare ta EU Kaja Kallas na kokarin daidaita alaka da kasashen yammacin Afirka
Babbar jami'ar hulda da ketare ta EU Kaja Kallas na kokarin daidaita alaka da kasashen yammacin AfirkaHoto: Wiktor Dabkowski/ZUMA/IMAGO

 A hirarta da tashar DW, babbar jami'ar hulda da kasashen ketare ta kungiyar Tarayyar Turai EU Kaja Kallas ta nunar da cewar suna goyon bayan tunkarar lamarin ta wata sigar ta dabam, musamman kan batun tattalin arziki. Ta ce: "Ina ganin cewar ya kamata mu magance matsalar da ke kawo rashin zaman lafiya tun daga tushe, wacce ita ce ta tattalin arziki. Muna kokarin taimakon Afirka, saboda makwabtanmu ne kuma matsalar makwabcinka taka ce. Sai dai muna kokarin kulla alakar da kowanne bangare zai amfana da ita, ga misali a bangaren makamashi da kayayyakin da ake sarrafawa da ake samunsu a Afirka."

Kaja Kallas ta nuna irin ci-gaba da za a samu huldar Kungiyar tarayyar Turai da kasashen yammacin Afirka, inda ta ce: "Muna maraba da taimakon da kasashen Afirka za su iya bayar wa a wannan alaka, mu kuma mu taimaka da fasahar da za a yi amfani da ita amma aikin zai kasance a Afirka za a yi shi. A wajenmu yana da matukar muhimmanci kayan aikin da ayyukan yin duka su kasance a Afirka, saboda idan da aikin yi babu batun gudun hijira. Matsalar rikicin 'yan gudun hijira za ta ragu sosai a Turai, saboda babu wanda zai so barin kasarsa idan yana da abun yi. A wajenmu muna fatan ganin kasashen Afirka sun bunkasa."

Koda yake Kallas ba ta ambaci Chaina ko Amurka ko kuma Rasha ba, sai dai kalamanta na nuni da abin da Hausawa ke cewa kowa ya yi zagi a kasuwa ya san da wanda yake yi.

Bakin haure na bi ta kasashen Sahel wajen isowa Turai

Da yake Kallas ta yi batu kan dakile kwararar bakin haure da 'yan gudun hijira, shugaban Shiri a yankin Sahel a Gidauniyar Konrad Adenauer ta Jamus Ulf Laessing na da ra'ayin cewa: "Akwai manyan hanyoyi biyu da 'yan gudun hijira ke bi daga yankin Kudu da Saharar Afirka wato Mali da Mauritaniya zuwa Tsibirin Canary, sai kuma daga Nijar zuwa Libiya su karasa Italiya. Saboda haka ba abin da za mu iya yi, sai dai tilas kungiyar EU ta ci gaba da tuntubar kasashen Afirka."

Shugabannin mulkin sojan Mali da Nijar da Burkina Faso
Shugabannin mulkin sojan Mali da Nijar da Burkina Faso Hoto: Mahamadou Hamidou/REUTERS

Sai dai ya ce akwai kalubale wajen gudanar da wannan aiki na yakar ta'addanci a yankin Sahel, inda ya ce: "Amurka ta shirya wani tsari na taimakawa Mali da Nijar da Burkina Faso, yadda za su yaki masu ikirarin jihadi. A al'adance Faransa ce ke da karfin fada a ji a yankin Sahel, sauran kasashen EU na rufa mata baya ne kawai. A yanzu da Faransa ba ta da ta cewa, sauran kasashen na fuskantar kalubale wajen shiga lamarin."

Karin bayani:Sahel: Kafa rundunar sintiri ta Turai

A nata bangaren, Dakta Lisa Tschörner wacce ta yi nazari kan tsare-tsaren Turai a Sahel mai taken "An Koma Gidan Jiya", a Gidauniyar Kimiyya da Siyasa ta Jamus, na da ra'ayin cewa ya kamata a koma tare da fadada alakar diflomasiyya da kuma tattaunawa da aka rage matuka shekaru biyu da suka gabata, domin rage rashin yadda da juna a kuma ware wasu muhimman fannoni da za su karfafa hulda tare.Nijar da EU na neman ja wa ta’addanci birki a SahelNijar da EU na neman ja wa ta’addanci birki a Sahel

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani