1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Ta'addanci

Nijar da EU na neman ja wa ta’addanci birki a Sahel

Gazali Abdou Tasawa MAB
May 16, 2023

Bisa taimakon Kungiyar Tarayyar Turai, Kwararru a harkar tsaro na kasashe 10 na Sahel da Sahara na duba rawar da fararen hula za su iya takawa a yaki da ta'addanci baya ga matakan soja da ake dauka don tinkarar matsalar.

https://p.dw.com/p/4RS4p
Sojojin Nijar na samun horo daga Eu don tinkarar ayyukan ta'addanciHoto: Issouf Sanogo/AFP/Getty Images

Kwararru kimanin 100 daga kasashen da suka hada da Nijar da Najeriya da Aljeriya da Libiya da Moritaniya da, Mali da Burkina Faso sun halarci taro da kungiyar EUCAP-Sahel ta shirya a birnin Yamai don nazarin hanyoyin shawo kan matsalar tsaro mai nasaba da ayyukan ‘yan ta'adda a kasashen Sahel da Sahara. A lokacin da yake jawabi a yayin bude taron, ministan cikin gida na kasar Nijar Hama Soule Adamou ya ce: " Idan muna son yin nasara a kan wannan matsala ta yaduwar hare-haren ta'addanci kan al'ummominmu, akwai bukatar hadawa da matakan farar hula a daura da na soja, ta hanyar kiyaye hakkin dan Adam da doka da oda, da kuma damawa da duk masu ruwa da tsaki a harkar tsaro."

Niger Niamey | Boris Pistorius in der Sahelregion
Ministan tsaron Jamus Boris Pistorius da takwaran aikinsa na Nijar Alkassoum IndatouHoto: Michael Kappeler/dpa/picture alliance

Ministan ya yi amfani da wnanan dama wajen neman hadin kan fararen hula wajen tinkarar ayyukan ta'addanci, inda ya kara da cewar: "A yankin Sahel akwai bukatar samar da fahimtar juna tsakanin al'umma ta yadda jama'a za su yi watsi da akidar tsattsauran ra'ayin irin wanda kungiyoyin ‘yan ta'adda ke yadawa. Don haka nake kira ga al'ummomi da jagororinsu su yi amfani da wannan dama domin bayar da gudunmawa ga bayar da kariya ga kasa daga wannan annobar ta'addanci."


Dalilin EU na kula da matsalar tsaro a Sahel

Kungiyar Tarayyar Turai ce ta dauki nauyin shirya wannan taro a karkashin shirin EUCAP-Sahel mai kula da taimaka wa kasashen Sahel a yaki da ta'addanci. Salvador Franca da ke zama jakadan EUi a Nijar ya ce: " Ta'addanci annoba ce wacce ba ruwanta da iyaka. Kuma mu nahiyar Turai makwabbta ne na kai tsaye da wannan yanki mai fama da ta'addanci. Abu ne da ke matukar tayar mana da hankali. Shi ya sa ba mu yi kasa a gwiwa wajen kawo tamu gudunmawa a wannan yaki ba."

Mali Unruhen Soldaten
Sojoji na bukatar hadin kan jama'a wajen yaki da ta'addanci a yankin SahelHoto: Sebastien Rieussec/Hans Lucas/IMAGO

Sai dai babban jami'in na Kungiyar Tarayyar Turai ya nuna bukatar hada kai da al'umma wajen ganin bayan ayyukan ta'addanci a sahel da Sahara. Ya ce: "Ba za a iya yin nasara kan wannan matsala ba matsawar babu hadin kan al'umma, ta hanyar shinfida adalci da aiwatar da ayyukan na inganta rayuwar al'umma da ci-gabanta. Za mu yi kokarin tattara fasahohi da dubarun yaki da ta'addanci, wadanda suka yi nasara a wasu kasashe ta yadda za a yi amfani da su a matsayin misali a sauran kasashen."

Kungiyoyin farar hula da 'yan siyasa na daga cikin wadanda suke bada gudunmawa, lamarin da Alassane Intinikar na jam'iyyar PNPD- Akalkassa, daya daga cikin mahalarta taron ya ce zai yi tasiri a fannin yaki da ta'addanci. Kwanaki uku za a share yini uku ana gabatar da makalolin guda 10 kan girman matsalar ta'addanci a Sahel ciki har da banbancin ta'addanci tsakanin Sahel da Turai, tare da fitar da shawarwari na tunkarar matsalar.