1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Rikice-rikiceChadi

Hari daga Sudan ya kashe mutum 18 a Chadi

Abdullahi Tanko Bala
March 19, 2026

Hukumomin Chadi sun ce fararen hula 18 sun mutu a wani harin jirgi mara matuki daga Sudan. Harin na baya bayan nan na daga cikin yaduwar yakin basasar da ke ci gaba a Sudan

https://p.dw.com/p/5AjwV
Wata mata yar gudun hijira akan iyakar Sudan da Chadi
Wata mata yar gudun hijira akan iyakar Sudan da ChadiHoto: Dan Kitwood/Getty Images

Gwamnatin Chadi ta sanar da cewa mutane 18 sun rasa rayukansu wasu da dama kuma sun sami raunuka a wani harin jirgi mara matuki da aka harbo daga Sudan wanda ya fada yammacin birnin Tine.

Garin na Tine ya na kan iyakar Chadi ne ta yammacin yankin Darfur na kasar Sudan.

Wani mai magana da yawun rundunar soji ya ce dukkan mutanen da suka mutu fararen hula ne.

Mutane a yankin sun ruwaito fashewar abubuwa guda biyu da suka fada kan masu halartar Jana'iza da kuma yara da ke wasa a kusa da wurin.