Erdogan ya soki gwamnatin Jamus | Labarai | DW | 25.07.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Erdogan ya soki gwamnatin Jamus

Shugaba Rajap Tayyip Erdogan na kasar Turkiyya, ya soki gwamnatin Jamus tare da yin Allah wadai da amfani da wadanda ya kira jami'ai da Jamus ke yi a kasarsa.

Shugaba Erdogan ya zargi Jamus din ne da kin amince masa, tare da wasu ministocin su yi jawabi a kasarta, yana mai mamakin yadda Jamusawa ke shiga Turkiyya suna kokari na raba kasar. Kalaman shugaban na Turkiyya dai na zuwa ne bayan tsare wani bajamushe dan fafutukar kare hakkin jama'a Peter Steudtner.

A farkon wannan watan ne dai 'yan sandan Turkiyya suka tsare Mr. Steudtner tare da wasu jami'an kungiyar nan ta Amnesty International a birnin Istambul. Jamus dai na daga cikin kasashen da suka hana Turkiyya damar yakin neman zabe a kasashensu, lokacin da Turkiyyar ke shirin zaben raba gardamar da ta yi a bana.