1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ebola: Jamus da wasu kasashen za su taimaka

February 24, 2019

Kasashen Jamus da Japan da kuma Australia sun kara yawan tallafinsu ga yaki da cutar nan ta Ebola, daidai lokacin da cutar ta halaka sama da mutum 500 a Kwango.

https://p.dw.com/p/3DzD9

UNICEF-Mitarbeiter reinigen sich während einer Schulung zur Infektionsprävention des Ebola-Virus in Juba im Südsudan
Hoto: Getty Images/A. Mcbride

Kasashen Jamus da Japan da kuma Australia sun kara yawan tallafinsu ga yaki da cutar nan ta Ebola, daidai lokacin da cutar ta halaka sama da mutum 500 a Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango.

Kasashen uku sun ce za su samar da dala miliyon 20 ga Hukumar Lafiya ta Duniya da ma Asusun Kula da Yara na Majalisar Dinkin Duniya, UNICEF saboda aikin.

Rabin kudaden dai za a yi amfani da su ne wajen daukar matakan gaggawa don yaki da cutar a Kwangon.

Ministan ma'aikatar kula da harkokin ci gaba a Jamus, Gerd Müller, ya ce dole ne su tashi don maganta matsalar cikin hanzari.

A shekarun 2014 da kuma 2015 ne, cutar ta Ebola ta halaka mutum dubu 11 a kasashen Gini da Laberiya da kuma Saliyo wadanda ke a yankin Afirka ta Yamma.