Duniya na takatsantsan ga juyin mulkin da aka yi a Thailand | Labarai | DW | 20.09.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Duniya na takatsantsan ga juyin mulkin da aka yi a Thailand

Kasashen duniya sun nuna damuwa game da juyin mulkin da sojoji suka yi a kasar Thailand. KTT ta yi kira ga sojojin da suka kifar da gwamnatin a birnin Bangkok da su gaggauta maido da mulkin demukiradiya a kasar. Daga birnin Washington kuwa rahotanni cewa suka yi jami´an gwamnatin Amirka sun sa ido suna dakwan irin ci-gaban da za´a samu a kasar ta Thailand. Ita kuwa ma´aikatar harkokin wajen Jamus a Berlin sanarwa ta fitar inda ta yi kira ga ´yan kasarta da a halin yanzu suke yawon bude ido a Thailand da su yi takatsatsan a kai komonsu musamman a birnin Bangkok. A kuma halin da ake ciki hafsan sojin kasar ta Thailand ya ce zai mika mulki ga wani sabon FM da za´a nada a cikin makonni biyu masu zuwa. Ya ce Basaraken kasar bai da hannu a juyin mulkin na jiya, wanda sojoji suka ce an yi ne don sake hade kan kasar. Yanzu haka dai FM Thaksin Shinawatra, wanda ke birnin New York lokacin da aka yi juyin mulkin, ya isa birnin London. Wani labarin da muka samu yanzu kuma na cewa Sarkin Thailand Bhumibol Adulyadej ya amince jagoran sojojin da suka yi juyin mulkin da ya shugabanci wata sabuwar majalisar mulki ta kasa.