Duniya Bai Ɗaya— Abokai Da Maƙiyan Afirka | Learning by Ear | DW | 22.01.2009
 1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Learning by Ear

Duniya Bai Ɗaya— Abokai Da Maƙiyan Afirka

Duniya Bai Ɗaya— Abokai Da Maƙiyan Afirka

Shirin Ji Ka Ƙaru zai duba yadda ci gaban duniya ya kasance a yau da kuma yadda ya shafi nahiyarmu ta Afirka. Shirin, zai baiwa masu saurarommu dama, ta sanin waɗanda suka taimaka wajen ƙere-ƙere da kuma waɗanda ci gaban ya fi shafa.

Shirin Ji Ka Ƙaru zai nuna yadda Duniya Bai Ɗaya, ta yi sanadiyar azirta wasu, wasu kuma ta ƙara talauta su.

Masu lura da yadda al’amuran yau da kullum a duniya ke faruwa, sun yi wani taro a Nairobi, Kenya, a shekara ta 2007 inda suka fito da ainihin gaskiyar abubuwan dake tauye cigaban ƙasashen nahiyar Afirka, suka ce ba wani abu ba ne, illa yadda duniya ta zamana bai ɗaya a kimanyace, wanda hakan ya kawo rashin ci-gaban Afirka, ya ƙara fatara da talauci. Duk da haka manyan ƙasashen duniya masu faɗa a ji, Babban Bankin Duniya da Asusun Ba da Lamuni suna masu ra’ayin cewa, Afirka ta buɗe ƙofarta domin a samu haɓakar kasuwanci da kuma ƙarfafa danƙon cinikayya da ƙasashen da suka ci-gaba domin su ma su amfana.

Fuskoki daban-daban

Shirin Ji Ka Ƙaru ba wai yana so ya nuna goyon baya ga wani sashe ba ne, a’a, yana ƙoƙarin nuna yadda duniya ta bambanta.

Masu ɗauko mana rahotanni sun zazzaga kuma sun yi hira da mutanen da suka bar gidajensu suka je neman arziki a birane da ƙasashen waje, za a nunawa masu sauraro irin yadda masu hazaƙa ta fannin kasuwanci suka amfana daga ci-gaban duniya bai ɗaya, da kuma yadda ilimin zamani ya kai nahiyar Afirka ta wajen ci-gaba a harkokin noma da kiwo.

An yi shirin na Ji Ka ƙaru a harsuna shidda, waɗanda suka haɗa da Ingilishi, Kiswahili, Faransanci, Hausa, Portuguese, da Amharic.

Shirin Ji Ka Ƙaru na samun gudunmuwa ne daga Ofishin hulɗa da ƙasashen waje na ƙasar Jamus.

Sauti da bidiyo akan labarin

 • Kwanan wata 22.01.2009
 • Mawallafi Zainab Mohammed
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink https://p.dw.com/p/DrEn
 • Kwanan wata 22.01.2009
 • Mawallafi Zainab Mohammed
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink https://p.dw.com/p/DrEn