1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Diaby: dan asalin Afirka a majalisar Jamus

Salissou Boukari
September 22, 2017

Karamba Diaby dan asalin kasar Senegal, wanda ke zaune a birnin Halle na Jamus ya jajirce na sake samun kujera a majalisar dokoki ta Bundestag, duk da tarin matsaloli da zagi da yake sha sabili da launin fatarsa.

https://p.dw.com/p/2kXsE
Deutschland Karamba Diaby
Hoto: picture alliance/dpa/S. Stache

Dan shekaru 55 da haihuwa, Karamba Diaby, ya kasance dan majalisar tarayyar Jamus a Bundestag tun daga shekara ta 2013. Ya kasance cikin wata tattaunawa tare da matasa na kungiya da ake kira Youth Initiative.Amma kuma yana fuskantar tarin matsaloli. Diaby ne dan majalisa na farko dan asalin Afirka a Jamus, Ya fuskanci matsala a yakin neman zabe mai cike da nuna kyama ta launin fata a shafukan sada zumunta a 'yan watannin nan.

Diaby ya ce "Idan mutum ya yayata manufofinsa na siyasa ta kafofin sada zumunta, wanda babu mai iya sauyawa, ana iya cewar muhawara na zahiri ba shi da wani tasiri. Tattaunawa da yawa da ake yi ta kafofin yada labarai na zamani, ba a yinsu ta hanyar da ta dace, amma kuma akwai kokarin tsoratarwa da kuma shiru na wakillan da aka zaba da ma sauran wasu wakillai na gwamnati."

Diaby wanda aka haifeshi a kasar Senegal, iyayensa sun rasu tun yana dan karami, kuma ya zo kasar Jamus ne a shekara ta 1985 inda aka bashi gurbin karo ilimi a fannin kimiyyar hada magungunna. Ya yi harshen Jamusanci kuma ya zabi garin Halle a matsayin birnin da ya zauna kuma ya auri wata daliba bajamusa, sannan ya soma kokawar neman aiki bayan kammala karatunsa. Diaby ya kudiri aniyar fuskantar kalubalen da jam'iyyar masu tsatsauran ra'ayi ta NPD.

Deutschland Schulz auf Sommertour in Sachsen-Anhalt mit Karamba Diaby
Schulz da ke takarar kujerar shugaban gwamnati a SPD a mara wa Diaby bayaHoto: picture-alliance/dpa/H. Schmidt

 Ya ce "Wasu mutane na yi min barazana, wasu kuma na zagina amma kuma suna cewa wai 'yancin fadar albarkacin baki ne, ni kuma na ce wannan ba shi da wani gami da 'yancin fadan albarkacin bak,i kuma ya saba wa kundin tsarin mulkin kasa."

Jam'iya mai kyamar baki ta AfD ta samu kashi 24 cikin 100 a zaben da ya gabata, amma kuma a cewar Karamba Diaby batun kyama ta launin fata da sauran miyagun kalamai sun kasance wani bangare na tarihi.

"Akwai wasu gungu-gungu na mutane da ba su bukatar tattaunawa, sannan kuma babu wasu shawarwari da suke bayarwa ta yadda za a iya inganta yanayin da al'ummomin ke ciki. Akwai wani babban tarin jama'a da ke da wayewa, a fannin demokaradiyya da taimakon juna, to wannan bangare wanda shi ne mafi yawa shi ne ke bani kwarin gwiwa."

Diaby ya samu babban takardar shaidar kammala karatu a wani nazarin da ya yi kan gurbacewar yanayi a lambuna na garin Halle, kuma bai taba barin birnin ba fiye da makonni hudu a jere, abin da ya sanya mutane ke daukansa a matsayin wani mai mutunci da rikon amana.