Dakarun duniya a Iraqi zasu kasance a kasar watanni 12 nan gaba | Labarai | DW | 29.11.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Dakarun duniya a Iraqi zasu kasance a kasar watanni 12 nan gaba

Kwamitin sulhu na MDD gaba dayansa ya amince da kara wa´adin aikin dakarun da Amirka ke wa jagoranci a Iraqi tsawon watanni 12 nan gaba. Hakan dai ya biyo bayan rokon da gwamnatin FM Iraqi Nuri al-Maliki ta yi ne na a taimaka mata wajen tabbatar da tsaro a lokacin da take kokarin gina dakaraun tsaron ta. Yanzu haka dai dakarun kasa da kasa zasu ci-gaba da kasancewa a Iraqi har zuwa ranar 31 ga watan desamban shekara ta 2007. A wani labarin kuma rundunar sojin Amirka ta ce dakarunta sun kashe wasu ´yan mata su 5 a wata musayar wuta da suka yi da wasu da ake zargi sojin sa kai a birnin Ramadi. Rundunar ta ce da farko wasu ´yan bindiga suka budewa sojojinta wuta daga rufin wani gini sannan su kuma suka mayar da martani.