COVID-19: Najeriya ta hana tarawi da tafsiri | BATUTUWA | DW | 21.04.2020
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

BATUTUWA

COVID-19: Najeriya ta hana tarawi da tafsiri

A karon farko a cikin tarihin Musulunci na shekaru ba adadi, kungiyar Jama'atul Nasarul Islam ta Musulmin Tarayyar Najeriya, ta ce ba za a yi sallar tarawi da tafsiri a lokacin azumi ba saboda annobar Coronavirus.

Nigeria Ramadan

Bana ba za a yi sallar jam'in tarawi da tafsiri lokacin azumi a Najeriya ba

Sallar tarawin ta nafila da tafsiri a lokacin azumin watan Ramadana dai, na zama na al'ada. Ba dai kasafai komai karfin 'yan mulki ke iya yanke hukunci a bisa batun addini a cikin Tarayyar Najeriyar kasar da ke takama da tisirin addin a tsakanin al'umma ba. To sai dai kuma daga dukkan alamu annobar COVID-19 tai nasarar mai da harkokin addinin ya zuwa baya, cikin kasar da ke fuskantar azumi da kuma ake shirin jingine al'adu na  lokacin  azumin.

Babu tarawi babu tafsiri

Wata fatawar  kungiyar Jama'atul Nasarul Islam  ta Musulmin Najeriyar dai, ta ce a bana kuma a karon farko da hankali zaya tuna, Musulmin kasar ba zasu gudanar da ibadojin al'ada na lokacin azumin a cikin bainar jama'a ba, da nufin kaucewa yada annobar cikin kasar.

Massen-Trauung in Nigeria

Babu zaman tafsiri a Masallatai

Farfesa Ibrahim Maqari na zaman daya a cikin malamai guda 10 da suka jagoranci fatawar da ke zaman irinta ta farko da kuma ke iya tasiri a cikin harkokin addini a kasar. To sai dai kuma  fatawar daga dukkan alamu na shirin hada kan daukaci na kungiyoyi na musulmi na kasar, da a baya ke rabe bisa banbanci na  akida a tsakaninsu. 

Hadin kan mabiya akidu

Dr Bashir Umar dai na zaman babban limami a masallacin Alfurkan da ke Kano, kuma a tunaninsa fatawar ta yi dai-dai, tun da dai al'adar ba ta  kai girman rai a cikin tsarin addini ba. Haka shi ma Ustaz Husaini Zakariya da ke zaman wani mai tafsirin a Masallacin Banex da ke Abuja fadar gwamnatin Njaeriyar. Tuni dai wasu malaman kasar suka dau hanyar kafafe na zamani da nufin isar da sakon da al'ummar kasar suke da bukata, a cikin sabon yanayin da kasar ke fuskanta a halin yanzu.

Sauti da bidiyo akan labarin