1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rasha na neman kyautata hulda da Afirka

Abdourahamane Hassane
October 24, 2019

Bangarorin biyu za su amfana da fanoni dabam-dabam kamar noma da makamashi, da hakar ma'adinai da makamashin iskar gas da ƙarafa, da ilimi, da harkokin zuba jari da kuma kimiyya.Hakan kuwa ya biyo bayan taron Sochi.

https://p.dw.com/p/3Rr4h
Russland | Afrika Gipfel in Sotschi
Hoto: Getty Images/AFP/A. Chol

A taron kwanaki biyu da aka yi tsakanin Rasha da kasashen Afirka, an cimma yarjeniyoyi da dama tsakanin sassan biyu na huldar kasuwanci da kuma al'amuran da suka shafi fasahar nukiliya da yawon bude ido. Rasha ta bayyana irin rawar da za ta taka a Afirka a cikin jadawalin taron. Za ta iya taimaka wa wajen bunkasar Afirka, ta fuskar tattalin arziki da tsaro, kamar yadda yake kunshe a jadawalin taron.