Taron hadin gwiwa tsakanin Rasha da Afirka
October 23, 2019Moscow dai na neman yin tasiri a wannan nahiya da tuni China da kasashen yammaci na Turai suka dade suna hulda a tsakaninsu.
Wakilai sama da 3000 da ke halartar taron na yini biyu da ke gudana a birnin Sochi, za su yi mahawadomin cimma yarjeniyoyi akan batutuwan da suka shafi makamashin nukiliya da hako ma'adinan karkashin kasa.
Shugaban kasar Masar AbdulFattah al Sisi da ke zama shugaban kungiyar tarayar Afirka na cikin manyan baki da ke halarta wannan taron, a yayin da ake saran dukkan kasashe 54 na nahiyar zasu samu wakilci, 43 daga cikinsu shugabanin kasashe ne ko gwamnatoci
Duk da cewa Rasha bata da wata babbar dangantaka da kasashe kamar su Najeriya da Ghana, suma shugabanninsu na halarta taron a cewar mai bada shawara a fadar Kremlin Yuri Ushakov.