Najeriya za ta sayo makamai daga Rasha | Duka rahotanni | DW | 22.10.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Najeriya za ta sayi makamai daga Rasha

Najeriya za ta sayo makamai daga Rasha

Shugaban Najeriya Buhari na neman sauya dabarun yaki da ta'addanci a Najeriya ta hanyar sabunta dangantaka da kasar Rasha domin sayo makamai masu tasiri don kawo karshen 'yan ta'adda musamman a Arewacin kasar.

Shugaba Buhari ya isa birnin Sochi, a Rasha

Shugaba Buhari ya isa birnin Sochi, a Rasha

Shugaba Muhammadu Buhari ya nuna alamun sauya dabarun diflomasiyyarsa zuwa ga kasar Rasha, cikin neman mafita daga rashin tsaron da ke lafawa ya kuma tashi musamman a arewa maso gabacin kasar.

Tarayyar ta Najeriya tana shirin cinikin makamai masu tasiri a yayin wata ziyarar da shugaban na tarayyar Najeriya ke yi a kasar Rasha.Fadar gwamnatin ta Najeriya ce dai ta bayyana makasudin wannan ziyarar ta shugaba Muhammadu Buhari, da ke zaman ziyararsa ta farko tun bayan hawansa mulki a 2015. Shugaban na Najeriya zai share kwanaki dai-dai har uku a cikin wannan taron da ke zaman irinsa na farko a tsakanin Russia da nahiyar Afirka, da kuma ke zaman alamun farkawa daga baccin Rashawan da ke da bukatar sabbin kawaye a Afirka.

Taron dai zai kalli dabarun sake maido da tsaro ne a kasashen nahiyar Afirka da dama, bayan batutuwa na ingantar al'adu da ciniki tsakanin Rasha da Afirka.Ta bangarorin kwaya izuwa matsalar ta'addanci ne dai Rashar ke shirin agazawa kasashen na Afirka ta hanyar dabaru na zamani da nufin tunkarar matsalar kamar yadda Malam Garba Shehu, kakakin gwamnatin Najeriyar kuma daya a cikin mahalarta taron a tsibirin Sochi da ke kasar.

“Har ya zuwa yanzu dai tarrayar Najeriyar na zaman jiran wasu jiragen Super Tucano da kasar ta yi ciniki a hannun Amurka amma kuma ba za ta kai ga karbarsu ba, sai kusan tsakiyar shekarar badi.To amma ana sa ran cewa cinikin na Rasha zai iya cike gibi ga bukatar tarrayar Najeriya, wanda da sannu a hankali ta ke kara fitowa fili cewar akwai bukatar karfin sama kafin a iya karar da masu ja da karfin ikon kasar da suka addabi tsakiya dama Arewa maso Yammaci.

Flt. Leutenant Aliko El-Rashid, wani masani ne na tsaron cikin Najeriya a halin yanzu, wanda ya ce cinikin na Rasha na iya sauya makomar yakin da kila ya kare cikin gaggawa in hali ya yi.“ Ko bayan batun ciniki da kila tasirin yakin, ana kuma kallon taka rawar Rasha a nahiyar Afirika na iya kara sha'awar manyan kasashen duniya a cikin harkokin nahiyar Afirika wanda a baya, a ke yi wa kallon bakar nahiya mai duhun da ba wanda yake son saka kai cikinta.

 

Sauti da bidiyo akan labarin