1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rasha na neman gidin zama a Afirka

October 23, 2019

Shugabannin kasashe da kwararru a fannin kasuwanci na Afirka na taron yini biyu a birnin Sochi na Rasha, wanda ke da nufin kulla alaka kan muhimman batutuwa tsakanin Rasha da kasashen Afirka.

https://p.dw.com/p/3RnpB
 Shugaban Kasar Mozambik Filipe Nyusi tare da Vladimir Putin
Shugaban Kasar Mozambik Filipe Nyusi tare da Vladimir Putin Hoto: Reuters/A. Zemlianichenko

Ana saran bangarorin biyu za su tabka muhawara kan al'amuran da suka shafi fannoni da dama kamar noma da makamashi, da hakar ma'adinai, makamashin iskar gas da ƙarafa, da ilimi, da harkokin zuba jari da kuma kimiyya. Ana fatan cimma yarjeniyyoyi a taron na Sochi a bangarori da suka shafi tashar nukiliya, da fasaha da yawon bude ido. Rasha ta bayyana irin rawar da za ta taka a Afirka a cikin jadawalin taron. Za ta iya taimaka wa wajen bunkasar Afirka, ta fuskar tattalin arziki da tsaro, kamar yadda yake kunshe a jadawalin taron.Yayin da aka bude taron, an baiyana Kasar Habasha a matsayin kasa ta baya-bayan nan da ta ci gajiyar shirin rancen raya kasa. A sakamakon hakan za' a yafewa kasar bashin da ake bin ta da ya kai dalar Amirka miliyan 160, wanda hakan zai bai wa kamfanonin Rasha da ke da sha'awar yin kasuwanci a Habashar damar zuba jari.