Bundesliga: Yiwuwar barin ′yan kallo shiga filin wasa | Labarai | DW | 04.08.2020
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Bundesliga: Yiwuwar barin 'yan kallo shiga filin wasa

Manyan rukunin kungiyoyin kwallon kafa guda biyu na Jamus, na nazarin yiwuwar bai wa mutane damar shiga kallon wasannin Bundesliga a watan Satumba, bisa wasu sharudda saboda annobar corona.

A karkashin tsarin da hukumar wasanni ta tarayyar Jamus ta gabatar a kakar wasanni da za a fara a ranar 18 ga watan Satumba, kungiyoyin sun amince da muhimman batutuwa guda hudu.

Shugaban hukumar Christian Seifert ya ce, yiwuwar barin 'yan kallon zai ta'allaka ne da hukuncin da gwamnati za ta yanke, kuma a shirye suke na amincewa da matakan kamar yadda ya faru a baya.

" A yanzu ba cikar fili da 'yan kallo ne ke da muhimmanci a Jamus ba. Za a cigaba da mayar da fifiko kan lafiyar al'umma, kuma bai dace mu sake shiga wani hadarin idan har zamu iya kauce masa ba. A lokaci guda kuma ba zamu nade hannuwanmu ba tare da daukar wani mataki ba".