Buhari zai sake yin takara a Najeriya | Labarai | DW | 15.10.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Buhari zai sake yin takara a Najeriya

Tsohon shugaban mulkin soja a Najeriya mai ritaya janar Muhammadu Buhari ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takara a ƙarƙashin babbar jam'iyyar adawa ta APC.

Buhari wanda ya tsaya takarar shugabancin ƙasar har karo uku ba tare da ya samu nasara ba, ya bayyana aniyar tsayawarsa a karo na hɗu a Laraban nan yayin wani gagarumin gangami da ya gudana a Abuja babban birnin Tarayayar Najeriyar. Yaƙar cin hanci da rashawa da tabbatar da tsaro shi ne batutuwan da Buhari ya sanya a gaba wajen neman jam'iyarsa ta APC ta tsayar da shi a matsayin ɗan takararta a babban zaɓen ƙasar da za a yi a shekara ta 2015 mai zuwa. A yayin ƙaddamar da takarar tasa tsohon shugaban mulkin sojan na Najeriya ya zargi gwamnati mai ci yanzu ƙarƙashin jam'iyyar PDP da Shugaba Goodluck Jonathan ke jagoranta da almundahana da kuɗaɗen al'umma da ma gaza samarwa da al'ummar abubuwan more rayuwa, baya ga jefa su cikin halin tasku sakamakon matsalar Ƙungiyar Boko Haram da ke gwagwarmaya da makamai kuma take cin karenta babu babbaka a ƙasar.

Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Abdourahmane Hassane