Bolivia ta bata rai da tsare shugabanta | Labarai | DW | 03.07.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Bolivia ta bata rai da tsare shugabanta

Evo Morales ya bar kasar Austria, bayan jami'an 'yan sanda sun gudanar da binciken jirginsa kan zargin tsohon ma'aikacin hukumar leken asirin Amurka, Edward Snowden yana ciki.

Wannan dai batu ne da a yanzu haka ya janyo cece-kucen diplomasiyya. Shugaban na Bolivia ya soki Turai da kakkausanar murya, dangane da hana jirginsa shiga sararin samaniyan wasu kasashen Turai a daren jiya. Morales da aka dakatar na tsawon awoyi 12 a filin saukar jiragen saman Vienna, ya fada wa taron manema labaru cewar, wannan wani yunkuri ne na jefa kasarsa cikin takaddama da Amurka. Tuni dai Jakadan Bolivia a MDD Sacha LIoreti ya gabatar da takardar koke wa babban sakataren majalisar Ban ki-moon, kan abun da ya kira saba wa dokar kasa da kasa. Ya ce karkatar da jirgin shugaban kasar cin zarafi ne ga Bolivia, kuma daidai ya ke da sace shugaban kasar. Tun a ranar talata da maraice ne dai, aka karkatar da jirgin da ke dauke da shugaba Morales, bayan tashinsa daga birnin Moscow, sao'i kalilan bayan shugaban ya ayyana yiwuwar bawa Snowden mafakar siyasa.

Mawallafiya: Zainab Mohammed Abubakar
Edita : Umaru Aliyu