Bayyanar cutar dan sakarau a Burkina Faso | Labarai | DW | 23.01.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Bayyanar cutar dan sakarau a Burkina Faso

Hukumomin kiyon lafiya sun sanar da mutuwar mutane biyar sakamakon cutar dan sankarau wadda kawo yanzu ta kama mutane da dama a kasar ta Burkina Faso.

default

Gidajen asibitoci dai sun sanar da bullar wasu cutuka da ke da saurin yaduwa a kasar ta Burkina Faso tun daga ranaikun 4 zuwa 10 ga wannan wata na Janairu kuma cikinsu an samu mutane akalla 63 da suka kamu da cutar dan sankarau, inda biyar daga cikinsu suka rasu a cewar sanarwar.

Hukumomin lafiyar kasar ta Burkina Faso dai sun sanar cewa, yawan wadanda suka kamu da cutar ya karu da mutum 29 idan aka kwatanta shi da na shekarar da ta gabata a daidai wannan lokaci. A shekarar da ta gabata dai kasashen irin su Nijar da Najeriya sun fuskanci babbar matsala dangane da wannan cuta ta dan sankarau.