Bayern ta lashe kofin kofuna na Jamus | Labarai | DW | 13.08.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Bayern ta lashe kofin kofuna na Jamus

Kungiyar Bayern Munich ta lashe kofin kofuna ko Super Cup na kasar Jamus a jiya Lahadi bayan da ta lallasa Kungiyar Frankfurt da ci biyar da babu.

Kungiyar Bayern Munich ta lashe kofin kofuna ko Super Cup na kasar Jamus a jiya Lahadi bayan da ta lallasa Kungiyar Frankfurt da ci biyar da babu. Dan wasan gaba na Kungiyar ta Bayern Munich Robert Lewandowski ne ya ci wa kungiyar tasa kwallaye uku daga cikin biyar. 

Wannan nasara da Kungiyar Bayern Munich ta samu kan Frankfurt na a matsayin ta daukar fansa daga kashin da Kungiyar ta Frankfurt ta ba ta da ci uku da daya a wasan cin kofin kalubale na kasar Jamus a ranar 19 ga watan Mayu. Kazalika wannan wasa ya kasance tamkar na sharen fage ga shiga kakar wasannin Bundesliga ta shekarar bana wacce za ta soma a ranar 24 ga wannan wata.

A kasar Spain ma dai kungiyar Barcelona ta lashe kofin kofunan bayan da ta lallasa kungiyar Sevilla da ci biyu da daya. Dan wasan baya na kungiyar ta Barcelona Gerard Pique da kuma dan wasan gaba Ousmane Dambele ne suka ci wa Barcelona kwallayen nata biyu.