Batun kudi zai mamayi taron NATO | Labarai | DW | 11.07.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Batun kudi zai mamayi taron NATO

Shugaba Trump ya saba fadin cewa kasashen Turai da Kanada na tafiyar hawainiya wajen kashe kudaden da suka dace a harkokin da suka shafi tsaro.

Batun abin da kowace kasa mamba a kungiyar NATO za ta kashe a fannin tsaro na zama babban jigo a taron da shugabanni mambobin wannan kungiya za su yi a wannan mako a birnin Brussels na Beljiyam, musamman a wannan rana ta Laraba da Alhamis, yayin da ake tsammanin Shugaba Donald Trump ya yi kalaman sakin bakin da ya saba a dangane da karin abin da kowace kasa za ta kashe kan harkokin sojanta.

Trump dai ya saba fadin cewa kasashen Turai da Kanada na tafiyar hawainiya wajen kashe kashi biyu cikin dari na abin da ke shigarwa kasashen a fannin na soja. Ya kara da jawabinsa na Twitter a ranar Litinin cewa Amirka ke kashe "kashi 90 cikin 100 ga abin da NATO ke bukata" sai dai babu wata hujja da shugaban ya dogara da ita wajen kaiwa ga wannan adadi.

Bayanan da kawancen ya tattara dai na nuni da cewa Amirka na da kasa da kashi 70 cikin 100 na abin da take kashewa. A 2018 dala miliyan dubu 706 daga dala tiriliyan daya da mambobin ke kashewa, Birtaniya ke bin Amirka sai Faransa da Jamus.