BATUN GIRKE DAKARUN MAJALISAR DINKIN DUNIYA A YANKIN DARFUR. | Siyasa | DW | 09.03.2005
 1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Siyasa

BATUN GIRKE DAKARUN MAJALISAR DINKIN DUNIYA A YANKIN DARFUR.

Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya, Kofi Annan, ya shawarci kwamitin sulhu na Majalisar da ya dauki matakan gaggawa, don girke dakarun kare zaman lafiya a yankin Darfur, saboda tabarbarewar halin tsaro da addabar mata a yankin.

Mata, `yan gudun hijira a yankin Darfur.

Mata, `yan gudun hijira a yankin Darfur.

Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya Kofi Annan ya bayyana wa kwamitin sulhu na Majalisar cewa, `yan mata da iyayensu mata ne suka fi huskantar addabar da mayakan kungiyar Larabawan nan ta Janjaweed ke ta yi wa al’umman yankin Darfur na kasar Sudan. Kofi Annan ya kara da cewa, hukumarsa na ta kara samun rahotanni game da kisa, da fyaden da ake ta yi wa mata da kuma kokkona gidajen da ake ta yi a wannan yankin. Sabili da haka ne yake ganin ya kamata, mambobi 15 na kwamitin sulhun, su dau matakan gaggawa don kawo karshen zub da jinin da ake ta yi a jihar ta yammacin Sudan.

Tun cikin farkon makon watan jiya ne, wani kwamitin bincike na Majalisar Dinkin Duniyar, ya gano cewa, dakarun gwamnati da mayakan kungiyoyin yankin na Darfur sun aikata munanan laifuffuka na take hakkin bil’Adama. Mafi yawan mambobin kwamitin sulhun Majalisar dai na yunkuri ne, dangane da wannan rahoton, na kai kararrakin masu aikata laifuffukan gaban kotun kasa da kasa na Majalisar Dinkin Duniya da ke birnin Den Haag na kasar Holland. Amma, matsalar da suke huskanta a nan ita ce, gwamnatin shugaba George W. Bush na Amirka, ta ki amincewa da wannan kotun.

A madadin haka, tana neman a kafa wata sabuwar kotu ne ta musamman, don gudanad da shari’a kan laifuffukan da aka aikata a yankin na Darfur #in kawai.

A cikin wannan rudamin ne dai, kungiyar ba da taimakon agajin nan ta Medecins sans Frontière ta buga nata rahoton, inda ta ce halin da `yan mata da iyayensu mata ke huskanta a yankin sai kara tabarbarewa yake yi. kungiyar ta ce tsakanin watan Oktoban bara zuwa Fabrairu na wannan shekarar, ta sami kararraki fiye da dari 3 na fyaden da aka yi wa mata a yankin, kuma ta kula da su a asibitocinta. Abin ban takaici shi ne, wannan danyen aikin ya shafi duk nau’in mata, masu shekaru tsakanin 12 zuwa 45 da haihuwa ne a yankin, inji kungiyar. Kuma duka matan da aka yi wa jiyya, sun ce kusan kashi 80 cikin dari na wadanda suka yi musu fyaden, wato mayakan kungiyoyin da ke samun daurin gindin gwamnatin Sudan ne ko kuma sojojin gwamnatin ma da kansu.

Kamar dai yadda Jan Egeland, mukaddashin shugaban Hukumar kula da `yan Gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniyar ya bayyanar, halin da ake ciki a Darfur din na nuna alamun gagarar magancewa. Habakar yawan addaba da tozarta wa mata da ake yi a yankin, ya kai matukar da gwamnatin Sudan din ma ta rasa gano bakin zaren warware matsalar, inji Egeland.

A wata sabuwa kuma, shugaban kungiyar SPLM, wanda kuma shi ne zai zamo mataimakin shugaban kasar Sudan, John Garang, ya nanata bukatar da akwai na kara yawan dakarun kasa da kasa a yankin na Darfur. Kamar yadda ya bayyanar wa maneman labarai:-

"In dai ba tare da sojojin ketare `yan ba ruwanmu ba, to zai yi wuya a shawo kan mayakan kungiyar nan ta Janjaweed, masu samun goyon bayan gwamnati. Sun gagara. Kwance musu damara da karfin soji ne kawai zai magance wannan matsalar. Ita dai gwamnati ba za ta iya daukan wani mataki ba, saboda ita ce ke ba su makamai."

To sai dai, yayin da kungiyoyin ba da taimakon agaji ke kira ga tura dakarun kare zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya zuwa yankin, John Garang na da nasa shirin. Bisa cewarsa dai:-

"Ina ba da shawarar a tura dakaru dubu goma-goma daga ko wane bangare, wato daga rundunar mayakana, da rundunar gwamnatin Sudan da kuma ta kungiyar Tarayyar Afirka, zuwa Darfur."

A halin yanzu kuwa, sojojin kare zaman lafiya na kungiyar Tarayyar Afirka dubu da dari 8 ne ke girke a yankin. Ana dai sa ran kara yawansu zuwa dubu 4. Sai dai, bisa dukkan alamu, rashin isassun kudade, da kafofin tsara shirin da kuma rashin makaman da suka dace ne, ke hana ruwa gudu wajen cim ma wannan manufar.

 • Kwanan wata 09.03.2005
 • Mawallafi Yahaya Ahmed
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink https://p.dw.com/p/Bvcp
 • Kwanan wata 09.03.2005
 • Mawallafi Yahaya Ahmed
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink https://p.dw.com/p/Bvcp