Bama bukatar sojoji a wurin zabe inji APC | Siyasa | DW | 19.02.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Bama bukatar sojoji a wurin zabe inji APC

Takaddama ta barke tsakanin 'yan dawa da jam'iyya mai mulki, inda yan adawan ke cewa basa bukatar tura sojoji a wuraren da ake kada kuri'un zabe, masu mulki na cewa halin rashin tsaro ya wuce wasa.

Kasa da yan makonni da komawa ya zuwa filin daga da nufin sake tabbatar da zaben shugabannin da za su ja ragamar Tarayyar Najeriya na tsawon wasu shekaru hudu,

Wata kotun dake garin Sakwatto dai ce ta fara haramta rawar ta soja yayin zabe, kafin kotun daukaka karar da ke nan a Abuja ta jaddada cikin bukatar ta adawa, da a baya ke zargin amfani da sojan da nufin murdiya a yayin zabe.

Masu adawar kasar ta Najeriya dai na neman tsaida aiki na jam'ian tsaron kasar ya zuwa na farin kaya, da 'yan uwansu 'yan sanda da kundin tsarin mulkin kasar ya tabbatarwa rawar takawa a zabukan.

Abun kuma da ya kaita aikewa da wasika zuwa ga shugaban kasar bisa nemansa da bin umarnin kotunan biyu na kyale soja cikin barikinsu yayin zaben.

Nigeria Wahlen 2011 Bild 2

Duk da cewar dai ya zuwa yanzun sojojin kasar ta Najeriya na jibge acikin akalla jihohi 32 cikin 36 dake kasar, a cewar Engineer Buba Galadima, da ke zaman daya a cikin 'yan kwamitin tabbatar da korar sojan daga rumfar zabe a cikin jam'iyyar APC, babu dama a garesu na tsoma baki balle sanya kafa a cikin shirin zabe.

“Babu kasa a duniya in ba inda ake kama karya ba, inda ake amfani da soja yayin zabuka. Wannan shi ya kai ni kasar Ghana, don inga yanda ake zabuka. In da babu soja, babu ma dan sanda mai makami yayuin zabe. Su kansu 'yan sandan da ke aikin zaben, suna karkashin umarnin shugaban zabe, shi zai ce su wane ku je wuri guda. Sai in har akwai hasumiya sai a kira wakilan jam'iyyu su sa hannu na amincewa, a tura 'yan sanda don tarwatsa hasumiyar. Shin me ya kai soja harkar zabe?”

Koma minene ya kai sojan kasar ta Najeriya harkar zabe dai, daga dukkan alamu dai a tunanin jam'iyyar PDP mai mulkin kasar, yanayi da ma barazanar da kasar ke fuskanta yanzu, ya sanya rawar ta soja tabbata a yayin zaben, a fadar Mohammed Hassan Shariff, da ke zaman jigo a cikin yakin neman zaben PDP na kasa.

“In ka duba kasar nan, ka sata a faifai ka kalli halin da kasar nan ke ciki, to ba soja ba hatta kwastam da Immigration, ya kamata su taka rawa cikin zabe. Ai rashin tsaro ne ya hana zaben can baya. Ai ina ga ba ma soja da kwastam ba, hatta 'yan banga ya kamata su shiga zaben nan don a yi lafiya a gama lafiya. Boko haram sun ce za su hana zaben nan, saboda haka dole ka hada duk ukun ka yi”

Ya zuwa yanzu dai sojan kasar ta Najeriya, su na saran baza tasirinsu har zuwa cikin shirin zabe na shugabannin, abun kuma da ya tilasta dage zabukan kasar zuwa karshe na watan gobe, bayan da sojan suka ce ba su da karfi na tabbatar da tsaro a ko'ina cikin kasar yayin zabe. To sai dai kuma a tunanin Festus Okoye da ke zaman shugaban kungiyar 'yan kallon zaben masu zaman kansu cikin kasar ta Najeriya, duk wata rawar da sojan ke iya takawa, to bai kamaci matsawa kusa da akwatin zabe koma rumfar yin zaben ba.

“In har soja na cikin shirin samar da tsaro a akalla jihohi 32 cikin kasar , za su iya kare manyan tituna da fararen hula, ko kum a tabbatar da cewar babu wanda ya aikata laifi yayin zaben, amma kuma bai kamata su kai ga tsayawa bayan turawan zabe ko a cikin rumfar zaben ba”

A baya dai masu adawa a kasar sun sha kai shaidun da ke tabbatar da hannun sojan a kokari na murde zabe a matakai daban daban. Har ya zuwa yanzu dai alal misali ana kace-nace bisa rawar sojojin wajen tabbatar da nasarar jam'iyya mai mulki a zaben gwamnan jihar Ekiti, a shekarar da ta shude.

Sauti da bidiyo akan labarin