Anyi garkuwa da wani dan Burtaniya a Najeriya | Labarai | DW | 31.03.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Anyi garkuwa da wani dan Burtaniya a Najeriya

A Najeriya yan bindiga sun sace wani maaikacin mai dan kasar Burtaniya a kudancin kasar.

Komishinan kula da muhalli na jihar Bayelsa Victor Akenge yace an sace mutumin ne a daren jiya.

Maaikatar harkokin wajen Burtaniyan ta tabbatar da wannan batu ta kuma ce tana tuntubar hukumomin Najeriya domin ganin an sako shi.

Kimanin yan kasar waje 70 ne aka sace tun farkon wannan shekara kodayake an sake da dama daga cikinsu amma har yanzu akwai wasu yan kasar Sin 2 da kuma dan kasar Netherlands guda daya.