1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Angela Merkel ta ja hankalin mata game da siyasa

October 23, 2021

Shugabar gwamnatin Jamus mai barin gado, Angela Merkel, ta nuna bukatar mata a Jamus su kara shiga cikin harkokin siyasa, musamman ma shiga a dama da su a harkokin jam'iyyu.

https://p.dw.com/p/425mI
Belgien | EU Gipfeltreffen in Brüssel - Angela Merkel
Hoto: Aris Oikonomou/REUTERS

A wata hirar da ta yi da jaridar Sueddeutsche Zeitung, Angela Merkel, ta ce tsarin tafiyar zamanin yau na bukatar mata su rika gogayya da maza a harkar siyasa akasin yanda abin yake a baya.

A cewarta muddin jam'iyyun siyasa na son tafiya da kowa, to lallai ne mata su kasance a matakansu na jagoranci gwargwadon yadda maza ke yi.

Shugabar gwamnati ta Jamus, wadda ta kasance mace ta farko da ta taba rike mukamin shugabancin gwamnati a kasar, ta kawo karshen takararta ne bayan mulkin shekaru 16 a jere.

Armin Laschet, wanda shi ne dan takarar jam'iyyar CDU ta Angela Merkel a zaben da ya gabata, ya bayyana aniyarsa ta jagorantar jam'iyyar kafin lokacin da zai yi adabo da siyasa.

Nan gaba ne dai jam'iyyar za ta sake zaben shugabanninta,