An yi zaman makoki a Ukraine | Labarai | DW | 05.03.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An yi zaman makoki a Ukraine

Al'ummar Ukraine da gwamnati sun gudanar da zaman makoki a gabashin kasar don nuna alhininsu bayan da wasu da ke aikin hakar kwal suka gamu da hadari a wajen da suke yin aiki.

Shugaban kasar Petro Poroshenko dai ya bada umarnin sako da tutocin kasar kasa-kasa yayin da majalisar dokokin kasar ta yi wani zama na musamman kan batun har aka yi tsit na minti guda don girmama wanda suka rasu, da ma soke dukannin wasu bukukuwa da aka shirya yi.

Hadarin dai ya yi sanadin rasuwar mutane 32. Yanzu haka dai rahotanni daga yankin da abin ya faru na cewar an kammala zakulo wanda wannan ibtila'i ya shafa yayin da wanda suka tsira ke cigaba da karbar magani a asibiti.