An kama mutane biyar a Jamus kan harin Paris | Labarai | DW | 17.11.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An kama mutane biyar a Jamus kan harin Paris

Uku daga cikin mutane biyar da aka kama a kusa da birnin Aachen 'yan kasashen ketare ne saboda alaka da hare-haren ranar Juma'a a kasar Faransa.

An kuma kama mutane biyar a garin Alsdorf na yamma a Jamus bisa dangantaka da hare-haren na birnin Paris da suka hallaka mutane 129. Garin na Alsdorf ya kasance kusa da birnin Aachen mai makwabtaka da kasar Holland. Mutanen sun hada da mata biyu da namiji daya. Sannan a kasar Beljiyam wani lauya ya tabbatar da cewa an cafke abokin daya daga cikin maharan.

Shugaba Francois Hollande na Faransa ya ce hare-hare birnin Paris da suka yi sanadiyar mutuwar kusan mutane 130 an kai su ne kan matasa da suka fito daga bangarorin rayuwa daban-daban. Kuma Faransa tana mayar da martanin da ya dace, inda kawo yanzu ta kai hare-hare masu yawa da tungar tsagerun kungiyar IS mai neman kafa daular Islama cikin kasar Siriya.

Mahukuntan Faransa suna ci gaba na bincike bayan kafa dokar ta baci kan wadanda ake zargi da ta'addanci da kuma matsanancin ra'ayi addinin Islama. Yayin jawabi ga zaman hadin gwiwa na majalisun dokokin kasar Shugaba Francois Hollande ya ce ta'addin ba zai wargaza Faransa ba, saboda Faransa za ta mayar da martani.