1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amurka ta yi watsi da karar 'yan Nijeriya akan Shell

April 17, 2013

Kotun kolin Amurka ta yi watsi da koken gurbata muhalli da take hakkin bil adama da wasu 'yan Najeriya suka shigar akan kamfanin mai na Shell a yankin Naija Delta.

https://p.dw.com/p/18IIQ
Umweltschäden durch Ölförderung (Shell) im Nigerdelta. Foto: DW/Muhammad Bello, Haussa Korrespondent from Niger Delta( Nigeria), 15.11.2011
Hoto: DW/M. Bello

Kotun kolin Amurka ta yanke hukuncin cewar, tsarin shari'ar kasar bashi da hurumin dora alhaki ko kuma akasin haka, dangane da ko katafaren kamfanin man petur na Shell ya taimaka wa gwamnatin Najeriya wajen azabtar da al'umma. Manyan alkalai guda tara na kotun kolin, sun yi watsi da karar da wasu 'yan Najeriya 12, dake zama dangin mutanen da gwamnatin mulkin sojin jihar Lagos ta zartar da hukuncin kisa akansu. Masu shigar da karar dai na zargin kamfanin shell da taimakawa tsohuwar gwamnatin kama karya ta mulkin soji wajen azabtar, aiwatar da kisan gilla da wasu nao'in laifuka da suka sabawa bil'adama tsakanin shekara ta 1992-1995, a yankin Niger Delta. Suna kuma zargin kamfanin na shell da tallafawa gwamnatin sojin wajen kame 'yan kabilar Ogoni 12, wadanda suka yi yunkurin dakatar da ayyukan hakar mai da ake a yankinsu cikin lumana, saboda illolinsa ga rayuwar al'ummar da muhalli. Shari'ar dai ta taso ne dangane da ko masu shigar da kara daga kasashen ketare zasu iya gurfanar da kokensu gaban kotun Amurka dangane da batu na take hakkin bil adama.

Mawallafiya : Zainab Mohammed Abubakar
Edita : Yahouza Sadissou Madobi