Amurka ta sake kama jirgin dakon man Iran a tekun Indiya
April 23, 2026
Rundunar sojin Amurka ta sanar da sake kwace wani jirgin dakon man Iran a wannan Alhamis a tekun Indiya, mai dauke da tutar Guyana, tare da shan alwashin ci gaba da dakile duk wata kafa da Iran din ke samun agaji ta ko ina.
Karin bayani: Iran ta ki amincewa da sake bude mashigar Hormuz
A sanarwar da shelkwatar tsaron kasar ta Pentagon ta fitar a wannan rana, ta ce jirgin dakon man mai suna Majestic X, ya fito ne daga Sri Lanka zuwa Indonesia, a kan hanyarsa ta zuwa China, kuma daidai wurin ke nan da ta kama daya jirgin mai suna Tifani.
Karin bayani:Iran ta bude wuta kan jiragen ruwa uku
Sai dai babu wani martani daga Iran kan wannan sabon kamu, wanda ya faru kwanaki uku bayan makamancinsa, kuma kwana guda bayan farmakin da dakarun juyin-juya-halin Iran suka kai wa wasu jirage uku a mashigin Hormuz, har ma suka kama biyu daga cikinsu.