Amurka ta baiwa Ahmedinejad Visa | Labarai | DW | 20.03.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Amurka ta baiwa Ahmedinejad Visa

Gwamnatin Amurka ta amince da bayar da Visa ga shugaban ƙasar Iran Mahmoud Ahmedinejad domin bashi damar zuwa New York don yin jawabi ga kwamitin tsaro na Majalisar ɗinkin duniya, yayin da a hannu guda kwamitin ke nazarin sabbin matakan takunkumi a kan Tehran bisa ƙin dakatar da shirin ta na makamashin Nukiliya. Kakakin fadar White Souse Sean McCormack ya shaidawa manema labarai cewa baki ɗaya Amurka ta amince da Visa 39 ga Ahmedinejad da mukarraban sa wanda ya haɗa da manyan jamián ƙasar Iran din su 12 da kuma jamián tsaro 26. Yace a halin yanzu ana cigaba da duba buƙatar wasu takardun izinin guda 33 na maáikatan jirgi da sauran jamiái. A dai halin da ake ciki Babu wata huldar jakadanci tsakanin Iran da Amurka wadda Amurkan ke ɗauka a matsayin ƙasar dake ɗaurewa ayyukan taáddanci gindi.