Amirka za ta baiwa Ukraine makamai | Labarai | DW | 13.12.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Amirka za ta baiwa Ukraine makamai

Ukraine ta yi maraba da kudurin doka da aka amince da shi wanda zai bada dama Amirka ta baiwa Kiev taimakon makamai daidai lokacin da ta ke rikici da 'yan aware.

Wannan doka da shugaban na Amirka Barack Obama zai sanyawa hannu na gaba zai bada damar aikewa Ukraine din kayan yakin da kudinsu ya kai dalar Amirka miliyan 350.

To sai dai mahukuntan Rasha da ake kallo a matsayin kanwa uwar gami a rikicin na Ukraine sun ce matakin na Amirka bai dace ba kamar yadda mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen Rashan Alexander Lukashevich ya shaidawa manema labarai.

Wannan dai na zuwa ne daidai lokacin da Amirka ta ce ta na shirin kara kakabawa Rasha karin wasu takunkumi, baya ga wanda aka sanya mata a baya.