Amirka ta ce za ta yafe wa Afghanistan duk basussukan da take binta. | Labarai | DW | 08.02.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Amirka ta ce za ta yafe wa Afghanistan duk basussukan da take binta.

Gwamnatin Amirka, ta ce za ta yafe wa kasar Afghanistan, duk basussukan da take binta. An dai kiyasci cewa, yawan basusskan ya kai dola miliyan dari da 8. Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Amirkan, Sean McCormac, ya fada wa maneman labarai a birnin Washington cewa, za bi ta kan rukunin nan na Paris Club ne wajen soke wannan bashin, kamar yadda aka saba. Wannan rukunin dai ya kunshi kasashe ne masu ba da lamuni. Kakakin ya kara da cewa, wasu kasashen rukunin, a cikinsu har da Jamus, su ma sun ce za su bi sahun Amirka wajen yafe wa Afghanistan basussukan da suke binta.