1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Labarin Wasanni: Alcaraz ya lallasa Djokovic

Suleiman Babayo LMJ
February 2, 2026

Mafi karancin shekaru a tarhin manyan wasannin Tennis na duniya, ya zama zakara a gasar da aka kammala ta Australian Open. Wanne hali ake ciki, a wasu wasannin lig da aka kara a kasashen Turai?

https://p.dw.com/p/57wyB
Carlos Alcaraz  | Australian Open | 2026 | Nasara | Carlos Alcaraz
Carlos Alcaraz ya lashe gasar Australian OpenHoto: Clive Brunskill/Getty Images

Za mu dauko shirin da wasan Tennis na Australiya da ya kawo karshe, inda Carlos Alcaraz ya samu nasara a bangaren maza tare da doka Novak Djokovic. Alcaraz mai shekaru 22 a duniya dan kasar Spain, ya zama mafi karancin shekaru da ya samu irin wannan nasara. Ita dai wannan nasara ta nuna yadda tasirin Novak Djokovic mai shekaru 38 da haihuwa dan kasar Sabiya, ya fara raguwa a fagen wasan na tennis a duniya. A bangaren mata kuma, Elena Rybakina ta doke Aryna Sabalenka a wasan karshe da 6–4 da 4–6 da 6–4.

Bundesliga | 2026 | Kora | SV Werder Bremen | Mai Horas da 'Yan Wasa | Horst Steffen
Horst Steffen mai horas da 'yan wasan kungiyar Werder Bremen da ta koraHoto: Kokenge/nordphoto GmbH/picture alliance

Kungiyar Werder Bremen da take matsayi na hudu daga kasan Teburin Bundesliga na Jamus kuwa, ta sallami mai horas da 'yan wasan kungiyar Horst Steffen bayan watanni bakwai kacal saboda yadda aka kwashe wasanni 10 a jere ana samun galaba kan kungiyar. Tuni aka nada Raphael Duarte da Christian Gross domin su maye gurbin mai horas da 'yan wasa da na wucin gadi, har zuwa lokacin da za a nada sabon mai horas da 'yan wasan. A sauran wasannin na Bundesliga da aka kara kuwa, an tashi kamar haka:

Cologne 1, Wolfsburg 0
RB Leipzig 1, Mainz 2
Bremen 1, Monchengladbach 1
Augsburg 2, St. Pauli 1
Hoffenheim 3, Union Berlin 1
Hamburger SV 2, Bayern 2
Eintracht Frankfurt 3, Bayer Leverkusen 1

Spaniya | 2026 | La Liga | FC Barcelona
Kungiyar kwallon kafa ta Barcelona ta yi nasara a karshen makoHoto: Haitham Al-Shukairi/AFP/Getty Images

A wasannin La Liga da aka kara a Spain, Barcelona ta bi Elche har gida ta ragargazata da 3 da 1. Ita kuwa Real Madrid da kyar da jibin-goshi bayan karin mintoci 10 a karshen wasa da kuma bugun da kai sai mai tsaron gida har da katin kora, kafin ta iya cinye Rayo Vallecano da 2 da 1. Sannan Betis da Valencia sun tashi 2 da 1.

Yanzu haka a jerin teburin na La Liga:

Barcelona        maki 55
Real Madrid        maki 54
Atletico Madrid    maki 45
Villarreal            maki 42
Espanyol            maki 34

Premier League | 2026 | Bukayo Saka | Arsenal
Kungiyar kwllon kafa ta Arsenal ta ci gaba da zama a saman teburin Premier LeagueHoto: Neal Simpson/Imago Images

A wasan Premier League da aka kara a Ingila, kungiyar Arsenal ta bi Leeds har gida ta doke ta da 4 da nema. Haka Chelsea ta doke West Ham da 3 da 2, yayin da Liverpool ta kassara Newcastle 4 da 1. Sannan Manchester United ta lallasa FC Fulham 3 da 2, kana Nottingham da Crystal Palace sun tashi 1 da 1.