Al'amuran Tsaro A gasar Cin Kofin Duniya
May 11, 2010Maganar tsaro na daga cikin batutuwan dake ci wa jama'a tuwo a ƙwarya, abin kuwa da ya haɗa har da ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta ƙasar Jamus, dangane da gasar ƙwallon ƙafa ta cin kofin duniya a Afirka ta Kudu. Ƙungiyar ƙwallon ƙafar ta Jamus, daidai da na sauran ƙasashe, zata halarci gasar ne tare da masu tsaron lafiyar 'yan wasanta. Sai dai kuma mai koyar da ƙungiyar wasan ƙwallon ƙafar ta Jamus Joachim Löw ya ce wannan ba wani mataki ne na musamman ake neman ɗauka ba.
A lokacin da yake bayani dai mai koyar da ƙungiyar ƙwallon ƙafar ta Jamus Joachim Löw ya ce ba za a yi wa 'yan wasan kariyar riga mai sulke ba. Dalilin wannan bayanin kuwa shi ne kasancewar jita-jitar sanya wata riga mai sulke ta haifar da ɓacin rai da ba'a a ƙasar Afirka ta Kudu mai masaukin baƙi, musamman kuwa ganin cewar wannan ba shi ne karo na farko da ƙasar ta karɓi baƙuncin wata gasa irin shigen wannan ba. An saurara daga bakin Theresa Bay-Müller daga ma'aikatar yawon buɗe ido ta Afirka ta Kudu tana mai bayanin cewar:
"Mun karɓi baƙuncin gasa iri daban-daban har 146 a 'yan shekarun baya-bayan nan kuma ba abin da ya faru."
Daga cikin waɗannan gasannin na ƙasa da ƙasa har da ta cin kofin zakarun ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa na nahiyoyi da aka fi sani da sunan confederation cup a shekarar da ta wuce ta 2009 da kuma gasar ƙwallon kirkit wadda aka ɗauke daga ƙasar Indiya zuwa Afirka ta Kudu sakamakon dalilai na tsaro lokacin zaɓen ƙasar ta Indiya. Amma fa duk da haka alƙaluma sun nuna cewar kimanin mutane 50 ake wa kisan gilla a Afirka da Kudu a kowace rana ta Allah. Horst Schmidt, mashawarcin Jamus a kwamitin shirya gasar ta ƙwallon ƙafa ta cin kofin duniya ya bayyana ra'ayinsa game da haka yana mai cewar:
"Duk wanda ya saba karanta waɗannan alƙaluma na miyagun laifuka a kowane wata zai yi zaton cewar miyagun laifukan sun yaɗu a ko'ina a saboda haka akwai wata babbar barazana wajen tafiya zuwa ƙasar. Wajibi ne a yi gyara game da haka."
Galibi dai waɗannan miyagun laifuka na faruwa ne a yankunan baƙar fata dake gefen manyan garuruwa da birane, wuraren da kuma a bisa al'ada masu yawon buɗe ido ba su kutsawa cikinsu. Alƙaluma ma dai sun nuna cewar kimanin Jamusawa dubu ɗari biyu da hamsin ne kan kai ziyara Afirka ta Kudu a duk shekara. A kuma lokacin gasar ta ƙwallon ƙafa ta cin kofin duniya ana sa ran adadin nasu zai zarce dubu ɗari uku. Dukkan waɗannan maziyarta za a kwashe su ne kai tsaye daga filin saukar jiragen sama zuwa masaukinsu kuma ofisoshin jakadancin ƙasashe dabam-dabam dake Afirka ta Kudu sun tanadar da bayanai a game da yadda ya kamata mutum ya riƙa kai da komo a garuruwa da birane na ƙasar. Vishnu Naidoo, kakakin 'yan sandan Afirka ta Kudun yayi alƙawarin cewar:
"Mun ɗauki nagartattun matakan tsaro akan dukkan hanyoyin dake sadarwa tsakanin filayen jiragen sama da masaukin baƙi, da masu sadarwa tsakanin masaukin baƙi da filayen wasa, ko tsakanin masaukin baƙi da wuraren yawon buɗe ido ko shaƙatawa. 'Yan sanda zasu barbazu ko'ina. Kimanin 'yan sanda dubu 41 muka tanadar akan manufa."
A baya ga haka 'yan sanda na ƙasashe da zasu yi wa ƙungiyoyin wasanninsu rakiya a wawware zasu samu cikakken rufa baya daga jami'an tsaron Afirka ta Kudu. Akan haka Horst Schmidt, mashawarcin Jamus a kwamitin shirya gasar ke cewar shi kam gabansa gaɗi bai ga wani abin damuwa game da lamarin.
Mawallafi: Ahmad Tijani Lawal
Edita: Muhammed Nasiru Awal