Aiki da yarjejeniyar tsagaita wutar Ukraine | Labarai | DW | 30.09.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Aiki da yarjejeniyar tsagaita wutar Ukraine

Kungiyar tarayyar Turai ta nemi da a yi aiki yadda ya kamata da yarjejeniyar tsagaita wuta da aka cimma tsakanin 'yan aware a gabashin Ukraine da kuma gwamnatin Ukraine din.

Kungyiar ta EU ta bayyana hakan ne bayan da jakadun kasashen da ke cikinta suka yi wani taro a yau don bin diddigin halin da ake ciki a Ukraine din inda mai magana da yawun kungiyar Maja Kocijancic ta ce an samu cigaba a wasu bangaren yarjejeniya da aka cimma a birnin Minsk amma kuma akwai bukatar ganin aiwatar da wasu sassa na yarjejeniya yadda ya kamata.

Ms Kocijancic ta ce nan gaba kadan kungiyar ta EU ta za duba yiwuwar sassauta takunkumin da kakabawa Rasha dangane da wannan rikici ko ma jingine shi baki dayansa in har yanayin da aka gani a kasa ya tanadi a yi hakan.