Afrika na nazarin sabbin dabarun yakar ta'addanci
April 22, 2024A cikin watanni bakwai na farkon shekarar da ta shude kadai dai akalla mutane 7,800 ne suka rasa ransu sakamakon aiyuka na ta'addancin da ke ta ruruwa a yankin Sahel.
Abun da ke tada hankalin 'yan mulki na kasashe na nahiyar Afrika da ke can a Abuja suna nazarin sababbi na dabarun hada kai da nufin tunkarar annobar.
Bazuwar kananan makamai, game da tsanani na talauci ko bayan baki na mulkin mulaka'u dai na taka rawa wajen yaduwa na kungiyoyi irin na su Boko ta haramun ta ISWAP da ragowar rassa na Al Qaidan da ke a nahiyar Afrika.
Shugabanni na kasashen Najeriya da Ghana da Benin da Togo, ko bayan wakili daga Chadi da ma kwarraru bisa harkar dai na shirin share kwanaki biyu suna nazarin hanyoyin dakile yaduwar ta'addanci da ma cike gibin da ya haifar da karuwar annobar.
Karin bayani: Mutane da dama sun mutu sakamakon harin 'yan bindiga a Neja
Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu da har ila yau yake zaman jagora na kasashen na Afrika bisa batun na ta'adda dai ya ce ko bayan batu na karfi na hatsi dai, Afrika na bukatar tunkarar annoba ta talauci da tabbatar da adalci kan kowa da nufin kare batun na ta'addanci da ke tashi ina dashi mai rai guda tara.
"Yaki data'addanci na bukatar kallon tsaf, dole ne mu warware ginshikin na ta'addanci, kamar na talauci, da wariya dama rashin adalci. To sai dai kuma hakan ba yana nufin hirar baka ba, dole ne mu yi aiki tare. A yanzu haka ta'addanci na zaman babbar barazana da ke rikida tana kuma samun hanyar daukar nauyin kanta".
Taron na Abuja dai na zuwa ne kasa da shekaru biyu da wani irin sa a birnin Accra, in da shugabannin yankin na yammacin Afrikasuke bullo da dabaru na dakile yaduwar ta ta'adda. To sai dai kuma sauyi na guguwa ta siyasa a cikin yankin dai ta kalli janyewar kasashe guda uku mafi tasiri a cikin yakin sakamakon juyin mulkin sojan.
Rikidewar Nijar da Burkina Faso da Mali zuwa ga mulkin soja dai a fadar Nana Akufor-Addo da ke zaman shugaban kasar Ghana, ta tilasta sauyin taku a bangare na kasashen yankin da ke ji har a tsakar ka daga annobar da ke barazana ga rayuwa ga makoma.
Karin bayani: Najeriya ta shirya hukunta masu daukar nauyin ta'addanci
"Abun takaici, janyewar Nijar da Mali da Burkina Faso daga ECOWAS domin kafa kungiyar kawancen Sahel ya jawo barazana ga inganci na dabarun birnin Accra. Kuma ana bukatar kallon sabo na kalubalen nan take da nufin nazarin irin mataki na gaba. Ghana a shirye take ta taimaka ta wannan fanni".
Duk da kauracewar ta kasashen guda uku dai kasashen yankin da yawa dai, sun ce suna ganin alamu na ci gaba cikin babban yakin. Nuhu Ribadu dai na zaman mashawarcin tsaro na tarayyar Najeriyar, da kuma ya ce kasar na fuskantar gagarumi na ci gaba a kokari na tunkarar annobar.
Tun daga shekara ta 2007 ne dai batun na ta'addanci ya fara yin tasiri a cikin yankin bayan bulla da kila tasiri na kungiyar Boko ta Haramun. To sai dai kuma rushewar tsohuwar gwamnatin Gaddafi da ita ce ake yi wa kallon ummul aba'isin bazuwa ta kanana na makamai a cikin kasashen ECOWAS.
Abun jira a gani dai na zaman tasirin tattaunawar ta Abuja a cikin tsanani na talauci da rashin aiyukan miliyoyi na matasan da ke zaman mafi yawa tsakanin al'ummar yankin.