1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tinubu ya yi watsi da biyan kudin fansa ga 'yan fashi

March 14, 2024

Gwamnatin Najeriya ta ce mai yiyuwa ta yi amfani da karfi wajen kubutar da mutanen da ake garkuwa da su, bayan da ‘yan fashin daji suka nemi kudin fansa a matsayin sharadin sakin ‘yan makarantar Kuriga da ke hannunsu.

https://p.dw.com/p/4dVmi
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya nuna alamun far wa masu sace mutane a kasar
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya nuna alamun far wa masu sace mutane a kasarHoto: Temilade Adelaja/REUTERS

Kwanaki uku da suka gabata ne wasu barayin daji suka nemi biyan famsar tiriliyan 40 na Naira domin sakin wasu mutane 16 da ke hannunsu. Sannan daga bisani wadanda suka sace 'yan makarantar Kuriga suka nemi a ba su Naira miliyan 1000 ko su halaka daliban cikin kwanaki 20 da ke tafe..Sai dai masu mulki na kasar na nuna alamun yunkurawa da nufin rage bacin suna da kima a rikicin satar 'yan kasar.

Karin bayani:Kaduna: Ko daliban da aka sace za su tsira? 

Sojojin Najeriya sun jima suna sa-insa da masu satar mutane a kasar
Sojojin Najeriya sun jima suna sa-insa da masu satar mutane a kasarHoto: Mosa'ab Elshamy/AP Photo/picture alliance

Abuja ta ce ba ta shirin biyan ko sisi da sunan fansa walau ta dalibai ko kuma rayuwar sauran 'yan Najeriya da ke hannun barayin. Maimakon haka, mahukuntan suka ce suna shirin gwada 'yar karfi in ya kama, da nufin tabbatar da cewar an saki daukacin 'yan kasar da ke a hannun barayin a fadar Mohamed Idris da ke zaman ministan labarai kuma kakaki na gwamnati.

Karin bayani: Kokarin magance tsaro a arewacin Najeriya

Ya zuwa yanzu dai, tarayyar Najeriyar na kallon ta’azzarar sace 'yan kasar domin neman kudin fansa. Sama da mutane 700 ne aka sace cikin tsawon mako daya ,a wani abin da ke kara tayar da hankali al’umma a kasar. Sai dai duk da ikarin da take yi a fili cewar babu babu fansa, amma ta karkashin kasa 'yan mulkin sun biya miliyoyin Nairori da nufin ceto kammamun walau cikin batun 'yan mata na Chibok ko kuma kammamun jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna, a cewar kyaftain Abdullahi Bakoji, kwarrare bisa batun tsaron.

Karin bayani:Najeriya: Najeriya: Ina kudaden fansa suke shiga?

Makarantun boko na cikin wurare da 'yan fashin daji suka fi kai wa hari a Najeriya
Makarantun boko na cikin wurare da 'yan fashin daji suka fi kai wa hari a NajeriyaHoto: AFP

Ko ina ake shirin kaiwa a shirin neman mafitar satar al’ummar? Da akwai sauran tafiya a tsakanin gwamnatin tarrayar Najeriya da ke tunkarar annobar rashin tsaro, a tunanin Dr Yahuza Getso da ke sharhi kan batun rashin tsaro. Amma iya samun nasara bisa batun tsaron na iya kaiwa zuwa ma'aunin farko bisa rawar gwamnatin da ke bukatar 'yan kasar su dora sabon fata a rayuwa da makoma.