1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya ta shirya hukunta masu daukar nauyin ta'addanci

Ubale Musa M. Ahiwa
March 20, 2024

A ci gaba da kokari na neman mafitar ta'addanci da ke kamari a Najeriya, kasar na shirin gurfanar da wasu mutane da kamfanoni har 15 bisa zargin samar da kudade ga masu ta'adda.

https://p.dw.com/p/4dwYx
Shugaba Bola Ahmed Tinubu na Najeriya
Shugaba Bola Ahmed Tinubu na NajeriyaHoto: Sunday Aghaeze/AP Photo/picture alliance

Akalla mutane tara da kamfanonin 'yan canji shida ne dai gwamnatin Najeriyar ta ce tana shirin mika wa kotu bisa zargin samar da kudade ga ayyuka na ta'adda

Wasu dai sun karbi kudin fansa suka mika wa barayin dajin, wasu kuma sun tura kudade a kai tsaye ga masu ta'addar daga kamfunan 'yan canji,  a yayin kuma da wasu ke cin moriyar kudaden kai tsaye, a fadar hukumar kula da hada-hadar kudi ta tarayyar Najeriyar NFIU.

Jerin sunayen dai sun hada da wani dan jaridar da ake zargi da karbar akalla Dalar Amurka dubu 200 tare da mika su ga masu  harin jirgin kasa da ke kan hanyar Abuja zuwa a Kaduna shekaru biyu baya,  da kuma wani da ake zargi da kai hari bisa wata coci a jihar Ondo, da ma wani dan ta'addan da ke da alaka da kungiyar al qaida da ke a Sahara.

Kasuwar canjin kudi a Najeriya
Hoto: picture-alliance/AP Photo/S. Alamba

To sai dai kuma a yayın da wasu da suka hada da dan jaridar ke hannu na  jami'an tsaron kasar, wasu a cikin 'yan laifin dai sun ba zakara sa'a, bayan fasa gidan yarin da ke garin Kuje.

Wannan ne dai karo na biyu da Abujar ke ayyana shiri na gurfanar da masu tu'ammalin kudi cikin batun na ta'adda, a tarayyar Najeriyar da ke kallon ta'azzarar satar al'umma a yanzu haka.

Batun na kudi dai ya zuwa yanzu na zaman iskar da ke tafi da harkokin ta'adda, walau a kungiyar ta Boko ta haramun ko kuma barayin dajin da ke dada nuna alamun karfi a sashen arewa maso yammacin kasar da ma tsakiyarta.

Kuma ko a cikin makon da ya shude dai tasirin na kudi a cikin harkar ya kunno kai inda wasu suka nemi Naira tiriliyan dai dai har 40 da sunan fansa bisa wasu mutane 16 da barayin suka kama a Gwanin Gora da ke cikin jiha ta Kaduna.

To sai dai kuma a yayin da barayin ke cin moriya cikin kudaden na haramun, ana kuma kallon jahilci cikin sana'ar canji na kudi na zaman na kan gaba wajen tafiyarwar harkokin na ta'adda. Najeriyar dai na zaman daya a cikin many ana kasashen dake gaba wajen hada hada ta kudade na ta'adda.