1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An kai wa sansanonin sojan Mali hare-haren ta'addanci

Abdoulaye Mamane Amadou
March 16, 2024

Hukumomi a kasar Mali sun tabbatar da kai wasu jerin hare-hare har guda uku mabanbanta a sansanonin sojojin kasar.

https://p.dw.com/p/4do4D
Hoto: Souleymane Ag Anara/AFP

A cikin wata sanarwar da ta fitar, ma'aikatar tsaron Mali, ta ce an kai jerin  hare-haren ne kan wasu sansanonin sojoji biyu da kuma wani shingen binciken jami'an Custom da ke wani kauye mai tazarar kilo mita akalla 100 daga kudancin birnin Bamako.

Sai dai rundunar tsaron kasar ta ce dakarunta sun yi nasarar fatattakar maharan, tare da kashe da dama daga cikinsu, kana kuma rundunar ta kara da cewa da dama daga cikin  'yan ta'addan sun samu mafaka a wani kungurmin daji.