Afirka a Jaridun Jamus: 04.06.2021 | Afirka a Jaridun Jamus | DW | 04.06.2021
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Afirka a Jaridun Jamus

Afirka a Jaridun Jamus: 04.06.2021

Matsayar ECOWAS ko CEDEAO ta dauka a kan Mali da batun kisan kiyashin da Jamus ta yi a Namibiya, sun dauki hankulan jaridun Jamus a wannan makon.

Ghana Accra| ECOWAS zur Lage in Mali | Nana Akufo-Addo

ECOWAS ko CEDEAO, ta mayar da Mali saniyar ware

A wannan mako za mu fara sharhi da labaran jaridun Jamus kan nahiyarmu ta Afirka da jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung wadda ta duba sabuwar rawar da kungyar Habaka Tattalin Arzikin Kasashen Afirka ta Yamma, ECOWAS ko CEDEAO ke takawa a wannan lokaci. Ta ce kungiyar ta yi ta kokarin shiga tsakani a kasar Mali. Bayan juyin mulki karo na biyu cikin kasa da shekara guda, ECOWAS ta dau gagarumin mataki. Ba ta yi wata-wata ba ta dakatar da Mali daga cikinta, ta kuma yi kira ga sojojin da suka yi juyin mulkin da su gaggauta nada firaminista farar hula. Ba kuma za a koma da kasar cikin ECOWAS ba, har sai ta shirya sabon zabe. Da ma gwamnatin rikon kwaryar da aka tumbuke, ta yi shirin gudanar da zabe a karshen wata Fabrairun 2022. Jaridar ta ce kungiyar wadda manufar kafuwarta a 1975 ita ce bunkasa tattalin arziki kasashe Afirka ta Yamma, yanzu tana taka rawa wajen daidaita al'amuran siyasa da al'adu da zamantakewa a kasashe mambobinta.

Flagge der Afrikanischen Union

Rikici ya barke a taron majalisar kungiyar Tarayyar Afirka kan shugabancin karba-karba

Yayin da ECOWAS ke fadada aikinta a yammacin Afirka, ita kuwa kungiyar Tarayyar Afirka a wani zama da majalisarta da ke Afirka ta Kudu ta yi, dauki ba dadi aka samu tsakanin 'ya'yan majalisar mai wakilai 250, lamarin da jaridar Die Tageszeitung ta kwatanta da raba kan kasashen Afirka. Jaridar ta ce bambancin ra'ayi tsakanin kungiyoyin yankuna dabam-dabam na Afirka, ya janyo dambacewa da barazanar kisa da yi wa wata 'yar majalisa feshin maganin kashe kwari. Jaridar ta ce abin bakin ciki ne yadda wannan abin kunya zai shiga cikin littattafan tarihi. Zaman majalisar an nuna shi kai tsaye a gidajen talabijin, an ga kuma yadda 'yan majalisar ke kai wa juna hari bisa sabanin ra'ayi kan bangaren da ya cancanci rike shugabancin majalisar. A yayin da wakilai daga Afirka ta Yamma da suka shugabanci majalisar sau biyu da na gabashin Afirka ke goyon baya a ci gaba da haka, su kuwa takwarorinsu na kudancin Afirka, na son a rika karba-karba kamar yadda ake yi a shugabancin kungiyar AU.

Deutsch-Südwestafrika Holzstich Hereroaufstand 1904/5

Jamus na kokarin kammala yin sulhu da Namibiya kan kisan kiyashi

Sulhu da Namibiya, wannan shi ne taken labarin da jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung ta buga a tsokacin da ta yi kan ta'asar da Jamus ta aikata a yankin Kudu maso Yammacin Afirka. Ta fara da cewa bai kamata tattaunawar da ake yi game da tarihin mulkin mallakar da Jamus ta yi a yankin da yanzu ya zama kasar Namibiya, ta kawo karshe bayan sanya hannu kan yarjejeniyar sulhu ba. Mahukuntan Jamus dai za su so a kammala yarjejeniyar da Namibiya, kafin karshen wa'adin wannan gwamnati. Tuni aka shirya ministan harkokin waje Heiko Maas zai je Namibiya domin rattaba hannu kan yarjejeniyar, shi kuma shugaban kasa Frank-Walter Steinmeier zai yi tattaki zuwa birnin Windhoek, inda a hukumance zai nemi afuwa dangane da kisan kare dangin da sojojin Jamus na lokacin mulkin mallaka suka yi ga al'ummomin Herero da Nama.

Tashe-tashen hankula a lardin Ituri na Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango, inji jaridar Die Tageszeitung tana mai cewa, tun bayan da Felix Tshisekedi ya dare kan kujerar shugabancin Kwango a 2019, lardin Ituri da Arewacin Kivu sun zama dandalin zubar da jini a kasar, inda mayakan kungiyar ADF da suka addabi yankin Beni ke yi wa farar hula kisan dauki dai-dai. A wannan shekarar kadai, mutane 65 aka yi wa kisan gilla a Ituri baya ga 'yan gudun hijira fiye da miliyan daya da suka tsere daga yankin.

Sauti da bidiyo akan labarin