Namibiya kasa ce da ke kudancin nahiyar Afirka. Tarayyar Jamus ta yi wa kasar ta Namibiya mulkin mallaka kafin Afirka ta Kudu ta mamaye ta a shekarar 1915.
Kasar ta samu 'yancin cin gashin kanta ne a shekarar 1990. Birnin Windhoek shi ne babban birnin kasar kuma yanzu haka kasar na kan tafarkin dimokradiyya tun bayan da ta samu 'yancin kai.