1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Salon rayuwaAfirka

El Nino na haifar da ambaliyar ruwa gami da fari

Cai Nebe SB/MAB
April 23, 2024

Nahiyar Afirka na fama da yanayin zafi na El Nino, wanda ya fara tasiri musamman tsakanin bara zuwa wannan shekarar. Yanayin da ke haddasa ambaliya da ke ta'adi, ya shafi kasashe irin Kenya da Tanzaniya da ke gabashi.

https://p.dw.com/p/4f5jp
Kamfan Ruwa
Kamfan RuwaHoto: Jhojan Hilarion/AFP/Getty Images

Kafin zuwan wannan lokaci dai yanayin zafin na El Nino, yanayi ne da galibin kasashe na yankin kudancin Amurka da Ecuador da Colombia da ma Bolivia ne aka sani suke fuskanta, inda har ta kai ga karancin ruwa ya zame musu alakakai. Hakan ne ma ya sanya daukar matakan adana ruwa da kuma rage yawan amfani da wutar lantarki a kasashen. Sakamakon kuma karuwar zafi a duniya, shi ma yanayin na El Nino ya ta'azzara matuka a yankunan da ake jin sa a jika. Yanayin da ke sabo a Afirka kuwa, ya sanya gwamnatoci a nahiyar tare da kungiyoyin kasa-da-kasa neman hanyoyin samun saukin sa ko ma shawo kansa.

Karin Bayani: Zimbabuwe na fama da farin da zai iya saka kasar cikin yunwa

Colombiya | Kamfan Ruwa
Kamfan RuwaHoto: Jhojan Hilarion/AFP/Getty Images

Kasar Zambiya da ke kudancin Afirka, tana neman dala miliyan 900 domin maganin fari da ta shiga mai kuma muni a tarihinta, sannan a gefe guda ta tsara hanyoyin kare rayukan miliyoyin 'yan kasar. Shugaban Zambiyar, Hakainde Hichilema ya ce rabin al'umar kasar da suka kai mutum miliyan 20 ne iftila'in ya El Nino ya shafa inda ya shafi gonaki da kuma harkokin kiwo.

Kasar ta Zambiya da ta ayyana matsalar fari a matsayin annobar da ta shafi kasa baki daya a cikin watan Fabrairu, na da dala milin 51 a hannu daga cikin miliyan 940 din da take bukata domin maganin yanayin. A Tanzaniya kuwa ambaliya sakamkon ruwan sama kamar da bakin masaki a farkon wannan wata na Afrilu ne ya yi jallin rayukan mutane 58 ciki har da kananan yara. A kasar Kenya ma haka labarin yake inda matsalar ke haddasa ambaliya mai muni.

Manyan cibiyoyin na kudi na duniya na kokari ne na tsara taswira ga kasashen duniya kan yadda za a hada karfi a magance matsalolin dumamar yanayi ko kuma sauyinsa. Ruwan sama mai karfi da ake ta shatatawa a sassa daban-daban na kasar Kenya cikin kwanakin nan, sun yi sanadiyyar mutuwar mutum 13, ya kuma raba mutum dubu 15 da muhalli.

Majalisar Dinkin Duniya ta samu alkawuran samun kudade na kusan kashi 75%  na dala biliyan guda da take bukata domin ayyukan jinkai a kasar Habasha da ke fama da rikicie-rikice da bala'o'in fari da kuma ambaliya. Sai dai kuma ta yi gargadin cewa ruwan sama mai karfin da ake gani a Kenya, na iya ci gaba har zuwa watan Yuli.