Abubakar Shekau ya ce ya na nan da ransa | Siyasa | DW | 02.10.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Abubakar Shekau ya ce ya na nan da ransa

Shugaban Kungiyar nan ta Boko Haram Imam Abubakar Shekau ya fito a wani sabon faifan bidiyo inda ya bayyana cewar ya nan da ransa sabanin ikirarin da sojin Najeriya suka yi cewar sun hallaka shi.

A cikin faifafan bidiyon mai tsawon mintuna 36, an nuna shugaban na Boko Haram cikin damara ta yaki inda ya ke sanye da kaki irin na soji da kuma takalmi sunke wanda sojoji suka saba sanyawa kana yana tsaye bayan wata mota inda ya ke harba bindiga.

Goodluck Jonathan Präsident Nigeria ARCHIV 2013

Shugaban Najeriya ya ce sun samun nasara a yaki da Boko Haram

Shekau ya musanta kisan da aka yi masa har ma ya ce ya nan da ransa inda ya ke cewar "Ina nan a raye, zan mutu ne kawai ranar da Allah ya dauki raina." Kazalika ya musanta ikirarin da sojin Najeriya suka yi cewar suna samun galaba a yakin da suke yi da kungiyar ta su.

Shugaban kungiyar ta Boko Haram ya kuma ce suna nan suna cigaba da fafutuka ta tabbatar da daular musulunci a yankunan da suke mamaye da su, inda ya kara da cewar suna aiwatar da hukunce-hukunce bisa tanadin da shari'ar musulunci ta yi.

Nigeria Sicherheitskräfte Boko Haram

Sojin Najeriya sun ce sun hallaka Shekau a makon jiya

A kwanakin baya ne dai rundunar sojin Najeriya ta ce ta hallaka wani mutum da ta ce shi ne ke fitowa a faya-fayen bidiyon da kungiyar ke fiddawa a matsayin Shekau, mutumin da sojin suka ce shigar sojan gona ya ke don su a cewarsu sun jima da kashe Abubakar Shekau.

'Yan Najeriya da dama dai na cigaba da tofa albarkacin bakunansu dangane da wannan batu inda dama daga cikinsu ke nuna rashin gamsuwarsu dangane da irin yadda ake samun bayanai marasa inganci kan yaki da Boko Haram daga rundunar sojan Najeriya.

Sauti da bidiyo akan labarin