Abu Namu: Matan Najeriya da sana'ar karuwaci a Jamus
January 13, 2020Talla
A kullum ana samun karuwar matan da ke zuwa Jamus daga Najeriya, akasarinsu wadanda aka yi simogarsu a cewar Barbara Wellner ta Solwodi, wata kungiya da ke taimaka wa 'yan matan da aka shigo da su ta hanyar fatauci da kuma tilasta su karuwanci.
A cewar Babara dai yawancin wadanda ke da hannu a irin wannan mummunan kasuwancin bil'adama mata ne, a wasu lokuta ma dangin yaran. A matsayin doka a harkar, sukan yi aiki a madadin sauran 'yan Najeriya da ke jan ragamar fataucin a irin kasashen da za a kai yara matan.
Wadannan masu fataucin mutane kan hari irin wadannan yara tun daga yankunansu na asali, sannan a yi karba-karba da su, daga bisani su iso cikin hannun manyan da ake kira "Madams" a Jamus