Ziyarar MDD a yanki Sahel | Labarai | DW | 20.10.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ziyarar MDD a yanki Sahel

Mambobi 15 na kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya na gunagar da ziyara a wasu kasashen kungiyar G5 Sahel, domin duba yadda za a kai ga girka runduna sojoji ta G5 Sahel.

UN Sicherheitsrat Nordkorea-Konflikt (picture-alliance)

Wani zaman taron Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya

Bisa yunkurin kasar Faransa da ke jagorancin kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya daga wannan wata na Octoba, mambobin 15 baki daya ne na kwamitin sulhun za su riyarci kasashen Mali da Mauritaniya da kuma Burkina Faso har ya zuwa ranar Lahadi wadanda suke mambobi a kashen na G5 Sahel gami da kasashen Nijar da Chadi.

Ministan tsaron kasar Mali Tiena Coulibaly ya tunatar cewa kungiyar ta G5 Sahel ta tsara kudadan tafiyar da rundunar ya zuwa Euro miliyan 423 amma kuma ya ce bisa wasu dalillai za iya rage wannan buri inda ya kara da cewa babbar mahawarar da ke a gabansu a yanzu haka ita ce ta ganin an soma wannan aiki wanda ta kamata a soma kafin karshen wannan wata na Octoba.

Rundunar ta G5 Sahel dai za ta kunshi bataliyar sojoji har guda bakwai da suka hada da biyu daga Mali biyu daga Nijar sannan bataliya dai-dai daga sauran kasashe mambobin kungiyar inda ake sa ran za ta samu cikakar girkuwa a watan Maris na 2018.